Sanatan jihar Borno ya bayyana halin ban-tsoron da ake ciki game da yakin Boko Haram

Sanatan jihar Borno ya bayyana halin ban-tsoron da ake ciki game da yakin Boko Haram

- Ali Muhammad Ndume ya koka da halin da ake ciki a jihohin Arewa maso gabas

- Sanatan ya bayyana cewa ‘Yan Boko Haram na neman dawowa Borno da kewaye

- ‘Dan Majalisar ya ce ka da ‘Yan ta’adda su hana a gina masu makaranta a Gwoza

A ranar Talata, shugaban kwamitin sojojin kasa a majaisar dattawa, Ali Muhammad Ndume, ya ja hankalin jama’a a kan halin da ake ciki a yakin Boko Haram.

Sanata Ali Muhammad Ndume ya bayyana cewa ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram su na taru wa a jihohin Arewa maso gabas na Borno, Yobe da Adamawa.

Punch ta fitar da rahoto cewa Ali Muhammad Ndume ya bayyana haka ne bayan ya gabatar da wani kuduri na neman a gina makarantar FCE a garin Gwoza.

KU KARANTA: A sa ido a kan 'Yan Boko Haram a Jigawa - Badaru

‘Dan majalisar ya na kokarin ganin gwamnatin tarayya ta kafa makarantar koyon ilmin karantar wa a Gwoza, Borno. Wannan kudiri ya kai mataki na biyu dazu.

Da yake jawabi a zauren majalisar, Muhammad Ndume, ya ce bai kamata a kyale ta’adin Boko Haram su hana a kafa wannan makaranta a kudancin Borno ba.

A cewar Sanata Ali Muhammad Ndume, duk da tarin mutanen da su ke yankin Borno ta Kudu da yake wakilta a majalisa, babu makarantar da ake horas da malamai.

Sanatan ya ce: “A makon jiya, an kashe sojoji 30 a babban titin garin Mainok. Jiya (Litinin), an rutsa sojojin wani gari da ke kilomita 30 da babban birnin Maiduguri.”

Sanatan jihar Borno ya bayyana halin ban-tsoron da ake ciki game da yakin Boko Haram
Sanatan jihar Borno ta Kudu, Ali-Ndume Hoto: www.guardian.ng

KU KARANTA: ‘Yan bindiga sun nemi su yi ram da 'Dan Majalisar dokokin jihar Katsina

“Sai da sojoji su ka tashi tsaye, amma mun rasa wani Manjo da wasu jami’ai biyu. A garin Rann, makamancin wannan lamarin ya auku.” Inji ‘dan majalisar dattawan.

“Matsalar da mu ke fuskanta a Borno da wasu bangarorin Yobe da Adamawa ita ce ta’addanci na neman sake dawowa, kuma wannan abin damuwa ne.” inji Sanatan.

Ndumi ya ce kafa makaranta a Gwoza zai kawo cigaba a jihar Borno da daukacin Arewa maso gabas.

A yau ne ku ka ji cewa babban malamin addini, Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana cewa 'yan ta'addan Boko Haram ne suka sace daliban jami'ar Greenfield ta Kaduna.

Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi magana game da daliban da aka yi garkuwa da su a ranar 20 ga watan Afrilu a lokacin da aka yi hira da shi a gidan talabijin AIT.

Asali: Legit.ng

Online view pixel