An biya N15m kuma an saki kasurgumin dan bindiga 1 a matsayin fansan daliban Afaka 27

An biya N15m kuma an saki kasurgumin dan bindiga 1 a matsayin fansan daliban Afaka 27

- Iyaye da gwamnatin jihar Kaduna sun bayyana farin cikinsu game da sakin daliban

- Tsohon shugaban kasa Obasanjo da Sheikh Ahmad Gumi suka taimaka wajen sakin daliban

- Obasanjo ya ce gwamnatin Jonathan da na Buhari sun biya kudin fansa a baya

Kwanaki 55 bayan sace dalibai daga makarantar fasahar gandun daji a Afaka, karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna, an saki sauran dalibai 27 dake hannun yan bindigan ranar Laraba.

A cewar Daily Trust, an saki daliban ne bayan an biya yan bindigan kudin fansa N15m tare da sakin wani kasurgumin dan bindiga.

An tattaro cewa yan bindigan sun ki sakin daliban duk da an biyasu kudin fansa saboda sun tubure sai an saki daya daga cikinsu da yan sanda suka kama.

An kai dan bindigan mai suna Laulu, Kaduna daga Kano ranar Talata.

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, da babban Malami Sheikh Ahmad Gumi ne suka kafa kwamiti na sulhu da yan bindigan.

Obasanjo da Gumi sun yi ganawa akalla sau biyu kan matsalar tsaron da ta addabi Arewacin Najeriya.

KU KARANTA: Daliban makarantar Afaka 27 sun dira hedkwatar yan sandan Kaduna

An biya N15m kuma an saki kasurgumin dan bindiga 1 matsayin fansan daliban Afaka 27
An biya N15m kuma an saki kasurgumin dan bindiga 1 matsayin fansan daliban Afaka 27 Hoto: DR Ahmad Mahmud Gumi
Asali: UGC

KU KARANTA: Ku yi hattara da yiwa Buhari barazana, Yan Majalisan APC sun yi raddi kan shirin tsige shugaban kasa

A bangare guda, Dr Ahmad Mahmud Gumi, ya bada nasa fatawar kan hukuncin biyan yan bindiga masu garkuwa da mutane kudin fansa don su saki mutum.

Wannan ya biyo bayan fatawar Limamin Masallacin tarayya, Farfesa Ibrahim Maqari.

Farfesa Ibrahim Maqari, a makon da ya gabata ya bayyana cewa addinin Musulunci bai amince da biyan masu garkuwa da mutane kudin fansa ba.

Amma Sheikh Ahmad Gumi a Tafsirin da ya gudanar ranar Laraba a jihar Kaduna, ya bayyana cewa kuskure ne haramta biyan kudin fansa ga masu garkuwa da mutane.

Shima ya kafa hujja da Hadisin Manzon Allah da ya ce an yafewa mutum wasu abubuwa guda uku, daga ciki akwai abinda aka tilasta mutum yi.

Sheikh Gumi ya caccaki Malaman da suka bada fatawar haramcin hakan saboda sun yi kawai don farantawa wasu rai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel