Daliban makarantar Afaka 27 sun dira hedkwatar yan sandan Kaduna
Daliban makarantar fasahar gandun daji FCFM Afaka a jihar Kaduna guda 27 da aka saki a ranar Laraba sun dira hedkwatar hukumar yan sandan jihar Kaduna.
Daliban sun sun dira hedkwatar cikin motocin Toyota Hiace guda biyu tare da rakiyan jami'an tsaro da motar asibiti.
A bidiyon da Channels TV ta dauka na daliban, da alamun gajiya da wahala tattare da su.
An hana yan jarida daukansu hoto saboda babu kaya a jikin wasu cikinsu.
Asali: Legit.ng