Biyan masu garkuwa da mutane kudin fansa ba haramun bane, Sheikh Gumi

Biyan masu garkuwa da mutane kudin fansa ba haramun bane, Sheikh Gumi

Shahrarren Malamin addini, Dr Ahmad Mahmud Gumi, ya bada nasa fatawar kan hukuncin biyan yan bindiga masu garkuwa da mutane kudin fansa don su saki mutum.

Wannan ya biyo bayan fatawar Limamin Masallacin tarayya, Farfesa Ibrahim Maqari.

Farfesa Ibrahim Maqari, a makon da ya gabata ya bayyana cewa addinin Musulunci bai amince da biyan masu garkuwa da mutane kudin fansa ba.

Farfesa Maqari ya kafa hujja da Hadisin Manzon Allah (SAW) inda wani mutum ya tambayesa shin ida barawo ya bukaci ya kwace kudinsa me zai yi, Manzon Allah ya fada fasa cewa kada ya bashi.

Amma Sheikh Ahmad Gumi a Tafsirin da gudanar ranar Laraba a jihar Kaduna, ya bayyana cewa kuskure ne haramta biyan kudin fansa ga masu garkuwa da mutane.

Shima ya kafa hujja da Hadisin Manzon Allah da ya ce an yafewa mutum wasu abubuwa guda uku, daga ciki akwai abinda aka tilasta mutum yi.

"Hadisin Abu Dhar Al-Ghifarry.... Allah ya yafe akan al'umman nan in tayi kuskure, ko ta mance ko aka tilasta ta. Saboda haka idan yan ta'adda suka kama ka ya zama dole sai ka biya kudi don ka tsiratar da kanka.... babu komai, kayi abinda Shari'ar Musulunci ta yarda da shi," Sheikh Gumi yace.

Biyan masu garkuwa da mutane kudin fansa ba haramun bane, Sheikh Gumi
Biyan masu garkuwa da mutane kudin fansa ba haramun bane, Sheikh Gumi Hoto: Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Asali: UGC

Sheikh Gumi ya caccaki Malaman da suka bada fatawar haramcin hakan saboda sun yi kawai don farantawa wasu rai.

Yace: "Muna ma malamanmu kashedi...An yi garkuwa da mutum ya ceci kanshi kuma kace ya yi haram? Sun yi abinda Allah da manzonsa suka yarda da shi."

Kalli bidiyon jawabinsa:

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng