Ku yi hattara da yiwa Buhari barazana, Yan Majalisan APC sun yi raddi kan shirin tsige shugaban kasa

Ku yi hattara da yiwa Buhari barazana, Yan Majalisan APC sun yi raddi kan shirin tsige shugaban kasa

- Ana musayar kalamai tsakanin Sanatocin PDP da na APC

- Yayinda marasa rinjaye ke barazanar tsige Buhari, na APC sun ce suna tare da shi

- Malamai da kwararru sun yi kira da Buhari ya tashi tsaye kan lamarin tsaro

Gamayyar Sanatocin APC a majalisar dattawa, a ranar Laraba, ta mayar da martani ga gamayyar marasa rinjaye bisa barazanar fito-na-fito da suka yiwa shugaba Muhammadu Buhari.

A ranar Talata, marasa rinjaye a majalisar dokokin tarayya, sun yi gargadin yin amfani da karfinsu wajen fito-na-fito da shugaba Muhammadu Buhari idan ya cigaba da saba kundin tsarin mulki.

Gamayyar marasa rinjayen sun lissafa jerin laifukan da Buhari yayi wanda za su iya amfani da su wajen tsigeshi.

Jagoran gamayyar kuma shugaban marasa rinjayen majalisar dattawa, Enyinnaya Abaribe, ya bayyana hakan a hira da manema labarai ranar Talata, a Abuja

Amma shugaban masu rinjaye, Yahaya Abubakar Abdullahi, ya yi martanin cewa shugaba Buhari na iyakan kokarinsa wajen magance matsalolin tsaro, riwayar jaridar Tribune.

Ya ce tabarbarewa tattalin arziki da cutar Korona ne suka haifar da rikicin da ake ciki a yanzu.

KU KARANTA: Daliban makarantar Afaka 27 sun dira hedkwatar yan sandan Kaduna

Ku yi hattara da yiwa Buhari barazana, Yan Majalisan APC sun yi raddi kan shirin tsige shugaban kasa
Ku yi hattara da yiwa Buhari barazana, Yan Majalisan APC sun yi raddi kan shirin tsige shugaban kasa Hoto: @NGRSenate
Asali: UGC

DUBA NAN: An biya N15m kuma an saki kasurgumin dan bindiga 1 matsayin fansan daliban Afaka 27

Sanata Abdullahi ya kara da daura laifin kan jam'iyyar adawa ta PDP inda yace shugabannin jam'iyyar sun ki zuba kudi wajen inganta tsaro tsawon shekaru 16 da suka mulki kasar.

"Muna Alla-wadai da tuhumar da suke yiwa shugaban kasarmu kuma bamu gani ba. Wannan karya ne kuma siyasa kawai. Shugaban kasa da hafsoshin tsaro na aiki tukuru kulli yaumin wajen tattauna hanyoyin magance matsalolin tsaron da suka addabi kasar," yace.

"A karshe, gamayyar Sanatocin APC na tare da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari yayinda muke cigaba da aiki domin magance matsalar tattalin arziki, tsaro, lafiya, da sauran matsalolin da suka addabi kasar."

A bangare guda, Kungiyar matasan Arewa mai suna Arewa Youths for Progress and Development (AYPD) ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi murabus saboda gazawar gwamnatin sa na magance rashin tsaro da tattalin arzikin da ke durkushewa.

Shugaban AYPD, Danjuma Sarki, ya bayyana cewa da wannan halin da kasar ke ciki a yanzu, gwamnatin Buhari ta gaza kuma ba za ta iya magance hauhawan matsalar rashin tsaro da tabarbarewar tattalin arziki ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel