Kungiyoyin sadarwa sun rantse sai Dr. Pantami ya ajiye kujerar Minista saboda ‘zargi’

Kungiyoyin sadarwa sun rantse sai Dr. Pantami ya ajiye kujerar Minista saboda ‘zargi’

- Kungiyar NATCOMS ta dage sai Dr. Isa Ali Pantami ya ajiye mukaminsa

- Shugaban NATCOMS ne ya bayyana wannan a jawabin da ya fitar a jiya

- Tun kwanaki aka huro wa Ministan sadarwan kasar wuta ya yi murabus

Masu amfani da kafofin sadarwa a karkashin kungiyar National Association of Telecoms Subscribers, sun yi kira ga Dr. Isa Ali Pantami ya yi murabus.

Jaridar Punch ta ce kungiyar ta bukaci Dr. Isa Ali Pantami ne ya sauka daga kan kujerar da yake kai na Ministan sadarwa da bunkasa tattalin arzikin zamani.

National Association of Telecoms Subscribers ta na so Ministan kasar ya ajiye kujerarsa ne duk da ya tsawaita wa’adin da aka bada na yin rajistar lambar NIN.

KU KARANTA: Buhari ya amince da murabus din Adeosun, ya maye gurbinta da Ahmed

Shugaban NATCOMS na kasa, Adeolu Ogunbanjo, ya yaba da kokarin Ministan na kara wa’adin rajistar, amma ya ce duk da haka akwai bukatar ya yi murabus.

Mista Adeolu Ogunbanjo ya na so Isa Ali Pantami ya rubuta takarda, ya bar kujerarsa domin a samu damar da za a gudanar da bincike na musamman a kansa.

A cewar shugaban wannan kungiyar, akwai bukatar Dr. Pantami ya yi koyi da tsohuwar abokiyar aikinsa, Kemi Adeosun wanda ta sauka daga kujerarta a 2018.

Kungiyar NATCOMS ta ce Dr. Isa Pantami zai iya koma wa kan kujerar ta sa, muddin aka gudanar da bincike, aka gano bai aikata laifin da ake zarginsa da shi ba.

KU KARANTA: Ni ba dan ta'adda bane - Pantami ya wanke kan shi

Kungiyoyin sadarwa sun rantse sai Dr. Pantami ya ajiye kujerar Minista saboda ‘zargi’
Isa Ali Pantami Hoto: NCC
Asali: Twitter

“A yanzu, ya sauka kamar yadda (Kemi) Adeosun ta yi, ya bada damar a cigaba da bincike. Idan har an wanke shi, sai ya koma kan mukaminsa.” Inji Ogunbanjo.

“Mun yaba masa da ya kara wa’adin rajista (na NIN), amma abin da ya dace shi ne ya yi murabus saboda a gudanar da bincike a kansa ba tare da an yi son-kai ba.”

Jawabin wannan kungiya ya kare da cewa: “Ya nuna halin girma, ya ajiye aikinsa kurum.”

A baya an ji shugaban majalisar wakilan tarayya, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila, ya musanta cewa ya yi fatali da yunkurin kiran a sauke Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami.

Da yake bayani a majalisa kwanakin baya, an rahoto Gbajabiamila ya na cewa bai dakatar da Hon. Elumelu lokacin da ya bijiro da maganar sauke Ministan ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel