Gbajabiamilla: Asalin abin da ya faru da aka tado batun Dr. Isa Pantami jiya a zauren Majalisa

Gbajabiamilla: Asalin abin da ya faru da aka tado batun Dr. Isa Pantami jiya a zauren Majalisa

- Majalisa ta ce ba a toshe korafin Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani ba

- Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya ce bai hana Ndudi Elumelu gabatar da kudirinsa ba

- Shugaban majalisar ya yi karin-haske game da abin da ya faru a zamansu na jiya

Shugaban majalisar wakilan tarayya, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila, ya musanta cewa ya yi fatali da yunkurin kiran a sauke Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami.

Jaridar The Cable ta rahoto Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya na cewa bai dakatar da Honarabul Ndudi Elumelu lokacin da ya bijiro da maganar ba.

Da yake karin-haske a ranar Alhamis, Femi Gbajabiamila, ya ce abin da ya faru shi ne ya ci gyaran Ndudi Elumelu na kawo batun ba tare da bin ka’ida ba.

KU KARANTA: Majalisa ta yi watsi da kudirin tsige Pantami daga kujerar Minista

Shugaban majalisar wakilan yake cewa babu bukatar muhawara a game da irin wadannan batutuwa da kwamitin majalisa yake bincike a kansu.

Da aka yi zaman yau, ‘dan majalisar jihar Borno, Ahmed Jaha, ya ja hankalin majalisa da cewa ana zargin majalisa da toshe yunkurin a taba Ministan.

Honarabul Jaha ya ce: “A matsayina na ‘dan majalisar nan, abin da na fahimta shi ne majalisa ba ta hana shugaba marasa rinjaye kawo wannan batun ba.”

Jaha ya kare shugabansa, Gbajabiamila ya na cewa: “Shugaban majalisa ya fada wa (Elumelu) ya bi ta hanyar da ta dace. Babu wanda ya taka masa burki.”

KU KARANTA: Rashin tsaro: Majalisar dattawa za ta gayyaci Dr. Isa Pantami

Gbajabiamilla: Asalin abin da ya faru da aka tado batun Dr. Isa Pantami jiya a zauren Majalisa
Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami
Asali: Facebook

Da yake yin martani, Femi Gbajabiamila ya yarda da abin da Jaha ya fada; “Kamar yadda ka yi bayani, Elumelu ya yi amfani ne da sashen doka ta shida.”

“Babu kudirin da aka kawo nan jiya.” Gbajabiamila ya bukaci ‘dan majalisar da ke da korafi a kan Ministan sadarwan, ya bi ta hanyar da doka ta bada dama.

Ana sa ran idan an koma zaman majalisa a mako mai zuwa, za a sake bijiro da maganar Ministan.

Shugaban kungiyar Izala, Sheikh Abdullahi Bala-Lau ya yi Allah-wadai da alakanta Ministan sadarwa, Isa Ali Ibrahim Pantami da kungiyoyin ‘Yan ta’adda.

Sheikh Abdullahi Bala Lau ya gabatar da hujjojin da su ke wanke Isa Ibrahim Pantami daga zargi, ya ce anya ba addini ake neman a yaka da sunan Ministan ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel