Yanzu Yanzu: Buhari ya amince da murabus din Adeosun ya nemi Zainab Ahmed ta maye gurbinta

Yanzu Yanzu: Buhari ya amince da murabus din Adeosun ya nemi Zainab Ahmed ta maye gurbinta

- Shugaba Buhari ya amince da murabus din Kemi Adeosun a matsayin ministar kudi

- Ya bukaci Zainab Ahmed, karamar ministar kasafi da tsare-tsare na kasa da tat a maye gurbin ta

- Femi Adesina ne ya bayyana hakan

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma’a, 14 ga watan Satumba ya amince da murabus din Kemi Adeosun a matsayin ministar kudi, jaridar The Cable ta ruwaito.

Shugaban kasar ya kuma amince da cewar Zainab Ahmed, karamar ministar kasafi da tsare-tsare na kasa da ta jagoranci ma’aikatar ba tare da bata lokaci ba.

Mai ba shugaban kasa shawara a kafofin watsa labarai, Femi Adesina ne ya bayyana hakan.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun kashe mutane 8 a jihar Nasarawa

Hasashe sun nuna cewa, Kemi Adeosun ta yi murabus ne bisa ga zargin rashin yin bautar kasan NYSC da ya wajaba kan kowani matashin Najeriya sannan kuma ta samu kwalin bautar na bogi.

Ministan ta yi murabus ne bisa ga yadda aka matsa mata lamba kuma yadda abin zai shafi zaben shugaba Buhari a 2019.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa hakan na zuwa ne shekaru da yawa bayan ta kammala jami’a.

Dokar Najeriya ta tanaji hukunci ga mutumin da duk ya ki zuwa aikin bautar kasa da gangan matsawar dai bai cika shekaru 30 ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel