Ni ba dan ta'adda bane; direba na da sakatariya ta Kiristoci ne, Pantami

Ni ba dan ta'adda bane; direba na da sakatariya ta Kiristoci ne, Pantami

- Ministan sadarwa na Najeriya, Pantami, ya musanta zargin samun matsala da Kiristoci

- Sabanin haka, ministan ya ce yana da kyakkyawar alaka da Kiristoci, cewa wasu daga cikinsu mambobin ma’aikatan shi mabiya addinin ne

- Pantami ya kuma musanta kasancewarsa tare da wasu kungiyoyin 'yan ta'adda

Isa Pantami, Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin zamani na Najeriyar, ya ce ba shi da wata matsala da Kiristoci, sabanin maganganun da ake yadawa a wasu rahotannin kafofin yada labarai.

Pantami wanda ya kasance sanannen malamin addinin Islama ya bayyana cewa yana da kyakkyawar dangantaka da Kiristoci, ya kara da cewa direbansa, sakatare da mai ba shi shawara kan harkokin fasaha duk kiristoci ne.

KU KARANTA KUMA: Fitaccen sanatan PDP ya bayyana dalilin da ya sa ba lallai ne a gudanar da babban zaben 2023 ba

Ni ba dan ta'adda bane; direba na da sakatariya ta Kiristoci ne, Pantami
Ni ba dan ta'adda bane; direba na da sakatariya ta Kiristoci ne, Pantami Hoto: @DrIsaPantami
Asali: Twitter

Wani rahoto da jaridar The Punch ta wallafa ya nuna cewa ministan ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da jaridar Peoples Gazette a ranar Juma’a, 16 ga watan Afrilu.

Pantami ya kuma ce bayanan da aka yi a baya kan kungiyoyin 'yan ta'adda da suka hada da Taliban da Al-Qaeda wasu mutane sun yi musu mummunar fahimta suna masu cewa yana da alaka da su (kungiyoyin' yan ta'adda).

An ruwaito shi yana cewa:

“Direba na shine Mai Keffi, mabiyin addinin Kirista. Ina kuma da Kirista, Ms Nwosu, a matsayin sakatariya na da Dr Femi, shi ma Kirista, a matsayin mai ba ni shawara kan harkar fasaha.

“Idan ba na son Kiristoci ko kuma ban dauke su a matsayin‘ yan uwana maza da mata ba, da ban dade ina aiki tare da su ba. Na dauki Krista fiye da Musulmai aiki a ma'aikatana saboda na yi imani da cancanta kan kabilanci."

Ministan ya sake nanata cewa ba shi da wata alaka da kungiyoyin 'yan ta'adda, inda ya kara da cewa ya yi shekaru yana wa'azin zaman lafiya da hakuri da addini.

KU KAARANTA KUMA: Na sauya masu tsattsauran ra'ayi sama da 1000 tare da koyarwar addinin Islama, Pantami ya fadawa 'yan Najeriya

A baya mun ji cewa Ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani, Isa Pantami, ya ce zarge-zargen cewa yana da alaka da masu tsattsauran ra'ayi karya ce kawai.

Pantami ya fadawa jaridar Premium Times a wata hira ta musamman a ranar Juma’a, 16 ga watan Afrilu, cewa mutanen da ke adawa da yadda gwamnati ke hada lambar NIN da lambobin wayoyi sune ke yada zargin.

Ya yi ikirarin cewa wasu tawaga sun dauki aniyar dakatar da manufar yin rajistar shaidar zama dan kasa ga dukkan ‘yan Najeriya da kuma wadanda ke zaune a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel