Amotekun Ta Sake Fatattakar Ƴan Arewa 137 Daga Dazukan Ondo

Amotekun Ta Sake Fatattakar Ƴan Arewa 137 Daga Dazukan Ondo

- Rashin tsaro a jihar Ondo ya tilasta wa jami'an tsaro na Amotekun fara korar baƙi daga jihar

- An kori baƙi da ke zaune a dazukan jihar ba bisa ƙa'ida ba an saka su a mota an mayar da su jihohinsu

- Shugaban hukumar Amotekun na jihar ya ce sun samu bayyanan sirri da ke nuna baƙi na shigowa dazukan jihar

Jami'an tsaro na hukumar Amotekun sun kori ƴan arewa da adadinsu ya kai 137 daga dazukan jihar Ondo.

A cewar jaridar Vanguard, waɗanda aka kora ɗin suna zaune ne a dajin Elegbeka da ke kan hanyar Ifon zuwa Owo.

Amotekun Ta Sake Fatattakar Yan Arewa 137 Daga Dazukan Ondo
Amotekun Ta Sake Fatattakar Yan Arewa 137 Daga Dazukan Ondo. Hoto: @RotimiAkeredolu
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Da Ɗuminsa: An Damƙe Wanda Ake Zargi da Ɗaukan Nauyin Kai Hare-Hare a Imo

Da ya ke bayani kan matakin da suka ɗauka kan ƴan arewan, shugaban Amotekun na jihar Cif Adetunji Adeleye ya ce cigaba da zama da mutanen ke yi a dazukan barazanar tsaro ne ga jihar Ondo.

Adeleye ya ce za a mayar da dukkan wadanda ke zaune a dazukan jihar ba bisa ƙa'ida ba zuwa jihohinsu na ainihi.

KU KARANTA: Abun Al’ajabi: Wata Mata Da Bata San Tana Ɗauke Da Juna Biyu Ba Ta Haihu a Jirgin Sama

Kalamansa:

"Mun samu bayannan sirri cewa mutane da dama suna kwararowa cikin dajin da ke hanyar Elegbeka zuwa Ifon a jihar. Mun shiga muka musu tambayoyi kuma galibinsu sunce daga arewa suka zo.
"Munyi bincike a kansu mun gano cewa suna haɗa baki da wasu ɓata gari a Ose domin a basu izinin zama a dazukan gwamnati wanda hakan ya saɓawa doka."

An daɗe ana kai hare-hare a jihar Ondo inda aka ce ƴan bindigan sukan ɓoye ne a dazukan jihar don shirya makircin su.

A wani labarin daban tsohon mataimakin shugaban kasa Mr Atiku Abubakar, a ranar Litinin, ya zargi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da musgunawa kafafen watsa labarai da yi wa yan kasa barazana idan sun bayyana ra'ayoyinsu.

Atiku ya yi wannan zargin ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter @atiku domin bikin ranar Yan Jarida na Duniya.

Ya bayyana cewa idan ana tauye hakkin mutane a mulkin demokradiyya, hakan zai kawo rashin jituwa tsakanin mutane da gwamnatin kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel