Abun Al’ajabi: Wata Mata Da Bata San Tana Ɗauke Da Juna Biyu Ba Ta Haihu a Jirgin Sama
- Lavinia Mounga ta fara nakuda a jirgi lokacin da take tafiya Hawaii ranar Laraba, 28 ga Afrilu
- Mounga da mijin ta basu san tana dauke da cikin ba tsawon watanni har sai da lokacin haihuwa yazo
- Bidiyon yadda lamarin ya faru ya yadu bayan da daya daga cikin fasinjojin jirgin ya dora a Tik Tok
Lavinia Mounga, da ta fito daga Utan, ta gamu da abu mafi ban mamaki a rayuwar ta bayan ta dauki ciki wata tara ba tare da sanin ta ba.
Ranar Laraba, 28 ga Afrilu, matar wadda ta hau jirgin sama tare da iyalan ta don tafiya Hawaii ta fara nakuda.
DUBA WANNAN: An Kama Soja da Harsashi Sama da 2000 a Tashar Mota a Maiduguri
Labarin Mounga ya yado bayan daya daga cikin fasinjojin jirgin, mai suna Julia Hansen, ya sanar da labarin a TikTok, yana cewa, 'an haifi jariri a wannan jirgin.'
A bidiyon, ana iya ganin mutane suna shagali tare da taya murna ga uwar bayan ta sauka lafiya.
Hansen ya bayyana cewa yana zaune a kusa da iyalan lokacin tafiyar, yayi ikirarin cewa ko mijin Mounga bai san tana dauke da juna biyu ba.
"Ga wanda ke mamakin yadda ta iya tafiya a jirgi bayan tana watan haihuwar ta. A kusa da mahaifin ta na zauna a jirgin, kuma yace su kan su basu san tana da ciki ba."
Likotoci da malaman jinya da dama wanda ke cikin jirgin sun taimaka mata wajen haihuwar.
KU KARANTA: Da Ɗuminsa: An Damƙe Wanda Ake Zargi da Ɗaukan Nauyin Kai Hare-Hare a Imo
Daya daga cikin malaman jinyar, Lani Bamfield, daga birnin Kansas ta sanar da labarin a shafinta na Facebook.
"Ga duk wanda ya ke son sanin yadda tafiyar mu zuwa Hawaii ta kasance, ga yadda ta kasance. Mun karbi haihuwar mai dauke da cikin sati 26-27 a bandakin jirgi, tare da malaman jinya uku masu karbar haihuwa, wani likita mai taimakawa da kuma likitan iyali; mun yi awa muku muna ta kokari kafin daga bisani ta haihu, amma jaririn da uwar suna cikin koshin lafiya."
Mahaifiyar ta sawa jaririn suna Raymond Kaimana kafin a kai su asibiti lokacin da jirgin ya sauka a Honolulu.
Asali: Legit.ng