Da Ɗuminsa: An Damƙe Wanda Ake Zargi da Ɗaukan Nauyin Kai Hare-Hare a Imo

Da Ɗuminsa: An Damƙe Wanda Ake Zargi da Ɗaukan Nauyin Kai Hare-Hare a Imo

- Jami'an tsaro sun yi babban kama a jihar Imo bayan an yi ta kai hare-hare a sassan jihar a baya-bayan nan

- An kama wani mutum mai suna Nnamdi Okafor da ake zargin shine ya ke daukan nauyin kai hare-haren

- An yi ta kai wa ofishohin rundunar yan sanda hari ana tafka ta'adi a jihar ta Imo cikin yn kwanakin nan

Jami'an tsaro a jihar Imo sun kama wani da ake zargin shine ke daukan nauyin kai hare-hare a jihar, an kama shi ne a Aboha-Ohi kusa da Assembly Owerri/Orlu road.

Binciken da Vangaurd ta yi a ranar Lahadi 3 ga watan Mayu ya nuna cewa sunan wanda ake zargin Nnamdi Okafor.

Da Ɗuminsa: An Damƙe Wanda Ake Zargi da Daukan Nauyin Kai Hare-Hare a Imo
Da Ɗuminsa: An Damƙe Wanda Ake Zargi da Daukan Nauyin Kai Hare-Hare a Imo. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yadda Muka Hana a Yi Wa Matasan Arewa 45 Kisar Gilla a Ondo, Amotekun

A cewar jaridar, Okafor wanda dan asalin garin Amanachi ne a karamar hukumar Orsu a jihar yana daya daga cikin wadanda ke daukan nauyin bata gari suna kai hare-hare.

An alakanta wanda ake zargin mai shekaru 42 da kashe-kashe, kona ofishin yan sanda da kai hari gidan gyaran hali a Owerri.

A wani rahoton da Sahara Reporters ta wallafa, an dade ana sa ido kan Okafor saboda zarginsa da alaka da hare-haren da bata gari ke kai wa.

Wata majiya da ta yi magana da jaridar ta bayyana cewa an kama Okafor, shugaban wani otel tun a watan Afrilu kan zarginsa da daukan nauyin yan daba da ke kai hare-hare a kudu maso gabas.

KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun Kashe Kwamishina, Sun Sace Shugaban Ƙaramar Hukuma a Kogi

Kama Okafor na zuwa ne kwana daya bayan jami'an tsaro a jihar sun kama yan bindiga 12 da ba a san ko su wanene ba.

An alakanta wadanda ake zargin da hare-hare a ofishin yan sanda da gidan gyaran hali na Owerri.

A wani labarin daban kunji wasu matasa a Daura, a ranar Alhamis 29 ga watan Afrilu sun kaddamar da kungiyar ta goyon bayan Dr Abubakar Bukola Saraki ya fito takarar shugabancin kasa a zaben 2023, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban kungiyar, Abubakar Nuhu Adam, ya ce sun yanke shawarar kafa kungiyar na goyon bayan tsohon shugaban majalisar ya yi takarar shugaban kasa ne saboda abin da ya yi da kuma abubuwan da ya ke yi wa matasa a kasar.

Hon. Adam ya bada misali dokar 'Not Too Young To Run' da aka aiwatar lokacin Saraki na shugabancin majalisa da kuma goyon bayan da ya bawa matasa su yi takarar kwamitin zartawar na jam'iyyar PDP da wasu sauransu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel