Hukumar Hisbah ta sallami jami'inta da aka kama da matar aure a Otal

Hukumar Hisbah ta sallami jami'inta da aka kama da matar aure a Otal

- Bayan watanni, hukumar Hisbah ta kammala bincike kan jami'inta da ake tuhuma

- An kama kwamandan ne da wata matar aure a unguwar Sabon Garin Kano

- Jami'in ya bayyana cewa 'yar uwarsa ce kuma taimakonta yake yi

Hukumar Hisbah reshen jihar Kano ta sallami Sani Nasidi Uba Rimo, daya daga cikin kwamandojinta da akayi zargin an kama da matar aure a Otal.

Kakakin hukumar, Lawal Fagge, ya tabbatar da hakan ranar Talata, Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce kwamitin da ta gudanar da bincike kan zargin da akayi masa ta kamasa da laifi.

Rimo, ya kasance babban jami'in da yake yaki da karuwai a jihar Kano. Amma an samu mishkila lokacin da aka yi zargin an kamashi da wata matar aure a Sabon Gari, a watan Febrairu.

Lokacin da aka tambayesa menene alakarsa da matar, an ruwaito cewa ya ce yar uwarsa ne, kuma ya ajiyeta a Otal ne don ta samu matsala da mijinta.

Sakamakon haka kwamanda Janar na Hisbah, Ustaz Harun Muhammad Ibn Sina, ya nada kwamiti don binciken lamarin.

DUBA NAN: Yan Boko Haram suka sace daliban Greenfield ba tsagerun yan bindiga ba, Sheikh Ahmad Gumi

Hukumar Hisbah ta sallami jami'inta da aka kama da matar aure a Otal
Hukumar Hisbah ta sallami jami'inta da aka kama da matar aure a Otal
Asali: Original

KU KARANTA: Ta yaya mutum zai gane ya dace da daren Lailatul Qadr? Tare da Dr Kabir Asgar

A bangare guda, jami’an hukumar Hisbah a jihar Kano sun kama wasu matasa da tsakar rana suna cin abinci, abinda ke nuna ba sa yin azumi.

An tattaro cewa matasan da aka damke sun hada da maza uku da kuma mata takwas.

A kowacce shekara hukumar ta Hisbah kan gudanar da irin wannan kame a cikin birni da kananan hukumomin Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel