Ta yaya mutum zai gane ya dace da daren Lailatul Qadr? Tare da Dr Kabir Asgar

Ta yaya mutum zai gane ya dace da daren Lailatul Qadr? Tare da Dr Kabir Asgar

- Mabiya addinin Islama na cikin kwanaki goma na karshe a watan Ramadana

- Malaman addinin sun kwadaitar da mabiyansu da su dukufa cikin Ibada a wadannan kwanaki

- A hira da wani babban Malami, ya yi bayani kan muhimmancin dacewa da daren Lailatul Qadri

Musulmai a fadin duniya a cikin kwanakin goma na karshe na wata mai alfarma ta Ramadana na gudanar da ayyukan Ibada domin dacewa da daren Lailatul-Qadri.

Domin sanin dalilin haka, Legit.ng ta tuntubi babban Malami, Dr Kabir Asgar, domin bayani kan muhimmancin wannan dare da kuma yadda aka gane an dace da daren.

Dr Kabir Asgar ya bayyana cewa Allah ya bayyana cikin Al-Qur'ani mai girma cewa wannan dare da Musulmai ke nema ya fi watanni 1000.

A bayanin Malamin, bautan Allah cikin daren tamkar bauta cikin watanni 1000 ne da kuma ladan da za'a samu a cikinsa.

"Daren Lailatul Qadri dare ne mai daraja kwarai da gaske, wanda Allah SWT yake cewa wannan dare darajarsa daya da wata dubu," Malamin yace.

"Ana iya samun daren ya dace da ranar 21, ko 23, ko 25, ko 27 ko 29. Dalilai suna karfafa ya fi zuwa a 27 fiye da sauran dararen."

"Dare ne wanda idan mutum ya dace da shi yana ibada, kamar ya yi dare dubu ne yana ibada."

DUBA NAN: Muna tare da shugaba Buhari, Hedkwatar Soji ta yi watsi da shawaran juyin mulki

Ta yaya mutum zai gane ya dace da daren Lailatul Qadr? Tare da Dr Kabir Asgar
Ta yaya mutum zai gane ya dace da daren Lailatul Qadr? Tare da Dr Kabir Asgar
Asali: Original

KU KARANTA: Wasu Malaman addini da tsaffin yan siyasa na son yiwa Buhari juyin mulki, Fadar shugaban kasa

Game da yadda mutum zai gane ko ya dace da dare, Dr Asgar ya ce akwai alamu da suka tabbata daga Manzon Allah kan alamun daren.

"Mutum zai iya ganewa, akwai alamu da ake iya ganewa. Za'a tarar da dare ne mai natsuwa, za aji wata natsuwa ta musamman wanda ya sabawa sauran dararrakun," yace.

"Sannan kuma idan gari ya waye, za'aga cewa rana ta fito amma ba tada zafi, sai dai haskenta amma ba zafi."

A bangare guda, Fitaccen malamin addinin nan, Muhammad Kabiru Haruna Gombe, ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya duba halin da al’umma su ke ciki.

A wajen darashin tafsirin da yake gabatar wa, Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe, ya yi kira ga shugaban Najeriya ya buda baitul-malin gwamnati.

Asali: Legit.ng

Online view pixel