Hukumar Hisbah ta kama matasa mata da maza da basa azumi a jihar Kano
- Hukumar Hisbah reshen jihar Kano ta damke wasu matasa da ta samu suna cin abinci da tsakar rana yayinda ake azumin Ramadana
- Wadanda aka kama din sun hada da maza uku da kuma mata su takwas
- Shugaban hukumar, Dr. Aliyu Musa Kibiya ya ce suna bincike kan wadanda aka kaman domin jin hujjarsu na kin yi azumin
Rahotanni sun kawo cewa jami’an hukumar Hisbah a jihar Kano sun kama wasu matasa da tsakar rana suna cin abinci, abinda ke nuna ba sa yin azumi.
An tattaro cewa matasan da aka damke sun hada da maza uku da kuma mata takwas.
KU KARANTA KUMA: Ta shiga matsala: An yi kuskuren tura mata N456m, ita kuma ta sayi gida da mota
A kowacce shekara hukumar ta Hisbah kan gudanar da irin wannan kame a cikin birni da kanana hukumomin Kano.
Shugaban hukumar, Dr. Aliyu Musa Kibiya ya ce suna bincikar wadanda basa azumin domin sanin dalilansu kamar yadda sashin Hausa na BBC ya ruwaito.
Azumin Ramada dai ya wajabta akan dukkan musulmi baligi ko baliga mai cikakken lafiya , sai dai idan akwai dalili mai ƙarfi ko uzuri ga mata masu haila ko tsoffi da ba sa jure yunwa ko ciwon gyambon ciki mai tsanani.
KU KARANTA KUMA: Ku je ku rarrashe shi: PDP ta tura Tambuwal, Obaseki da Saraki zuwa Cross River don ganawa da Ayade
A wani labari na daban, wata Baiwar Allah mai suna Lubna Ali ta jawo abin magana bayan ta bayyana irin tsananin soyayyar da ta ke yi wa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Lubna Ali a shafinta na Twitter, ta bayyana cewa a dalilin kaunar da ta ke yi wa Madugun Kwankwasiyya, ta ki amsa tayin aure da wani ya yi mata.
Wannan budurwa ta yi magana da jaridar Sahelian Times inda ta sake tabbatar da cewa ba za ta taba auren duk saurayin da bai ganin mutuncin gwarzonta ba.
Asali: Legit.ng