Yan Boko Haram suka sace daliban Greenfield ba tsagerun yan bindiga ba, Sheikh Ahmad Gumi

Yan Boko Haram suka sace daliban Greenfield ba tsagerun yan bindiga ba, Sheikh Ahmad Gumi

- Sheikh Ahmad Gumi ya saki sabuwa game da satan daliban Greenfield

- Yan bindigan sun yi barazanar kashe daliban idan ba'a biya kudin fansa N100m ba

- Gwamnatin jihar Kaduna ta ce ba zata yi sulhu da su ba kuma ba zata biya diyya ba

Babban malamin addini, Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana cewa yan ta'addan Boko Haram ne suka sace daliban Greenfield dake Kaduna ba yan bindiga ba.

An yi garkuwa da daliban ne a ranar 20 ga watan Afrilu 2021, a makarantarsu dake Kaduna.

Tun lokacin aka yanke cewa yan bindiga masu garkuwa da mutane ne suka sace yaran.

Amma a ranar Talata, Sheikh Ahmad Gumi a hirarsa na AIT ya bayyana cewa bincike ya nuna yan ta'addan Boko Haram suka yi garkuwa da yaran.

Yayinda aka tambayeshi shin yana da tabbacin yan Boko Haram ne, yace: "Tabbas kam. Yayinda muka yi kokarin bibiyansu domin yi musu magana, wanda muka tuntuba wanda shi ma Fulani ne sun yi masa barazana."

"Sun ce idan ya cigaba da damunsu zasu kamashi kuma shi kansa sai ya biya kudin fansa kafin a sake shi."

"Kuma shugabansu dan Jalingo ne. Ba irin Fulanin da muke dasu a nan bane. Saboda haka akwai matsalar rikicin Arewa maso gabas a nan kuma ya kamata muyi gaggawa. Bamu da lokaci."

KU KARANTA: Ku Ƙara mana Lokaci kar ku kashe 'yayan mu, Iyayen Ɗalibai sun Roƙi yan Bindiga

Yan Boko Haram suka sace daliban Greenfield ba yan tsagerun bindiga ba, Sheikh Ahmad Gumi
Yan Boko Haram suka sace daliban Greenfield ba yan tsagerun bindiga ba, Sheikh Ahmad Gumi Hoto: Sheikh Ahmad Gumi
Asali: UGC

KU KARANTA: An bankado badakalar kimanin N40bn a kasafin kudin 2021 da gwamnatin Buhari tayi

A bangare guda, daya daga cikin daliban da aka sace a jami’ar Greenfield da ke jihar Kaduna ya kubuta daga hannun 'yan bindiga.

Duk da cewa har yanzu ‘yan sanda da hukumomin gwamnati ba su tabbatar da hakan ba, mahaifiyar daliban, Lauritta Attahiru ta tabbatar da sakin danta ga gidan Talabijin na Channels, a ranar Talata.

Amma duk da haka ta ki bayar da cikakken bayani game da yadda aka saki dan nata kuma an biya fansa ko a'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel