El-Rufai: Kungiyar Musulmai ta fito ta yi magana a kan karin kudin makarantu, ta ce da sake

El-Rufai: Kungiyar Musulmai ta fito ta yi magana a kan karin kudin makarantu, ta ce da sake

- Kungiyar Musulman Najeriya ba ta goyi bayan karin kudin karatu a Kaduna ba

- Shugaban MSS na jihar Kaduna, Dr. Shehu Salihu Umar ya fitar da wani jawabi

- MSS ta roki Gwamnatin Kaduna ta sassautawa al’umman da talaka su ka fi yawa

Kungiyar Musulman Najeriya watau MSS, sun soki matakin da Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya dauka na kara kudin karatu a makarantun jiha.

A wani jawabi da shugaban kungiyar MSS na reshen jihar Kaduna, Malam Shehu S. Umar ya fitar, ya yi kira ga gwamnati ta janye matakin da ta dauka.

Shehu Salihu Umar ya yi wa jawabinsa da ya fitar a ranar Juma'a take da: “MULTI-FOLD INCREASE IN SCHOOL FEES OF HIGHER INSTITUTIONS OF KADUNA STATE GOVERNMENT: A CALL FOR URGENT REVERSAL OF THE UGLY POLICY.”

KU KARANTA: Kaduna: ‘Yan siyasa sun gagara cin jarrabawar shiga takara a APC

MSS ta ce ta sa ido a kan abubuwan da su ke wakana a jihar na yin karin kudin karatu a manyan makarantu, ta ce hakan zai kara jefa jama’a a cikin kunci.

Kungiyar ta MSS ta ce ta ji hujjojin da gwamnati ta bada na yin karin, amma talakawa ba za su iya daukar dawainiyar biyan makudan kudin da aka sa ba.

“Matsakaicin ma’aikacin gwamnatin jihar Kaduna da ke karbar N50, 000 a wata, sai ya adana albashin watanni uku kafin ya biya kudin makarantan yaro.”

Duk mai ‘ya ‘ya biyu a makaranta, sai ya yi watanni shida ya na tari, kafin ya hada kudin makaranta.

KU KARANTA: ‘Dan Majalisar Katsina ya kubuta daga hannun Masu garkuwa da mutane

El-Rufai: Kungiyar Musulmai sun fito sun yi magana a kan karin kudin Makaranta
MSS Kaduna Hoto: Facebook / Shehu Salihu Umar
Asali: Facebook

Amir, Shehu Umar ya bayyana cewa: “Babu adalci idan gwamna ya kawo gyaran da zai jefa akasarin al’umman da talakawa ne a cikin mawuyacin hali.

“Mafi yawan wadanda su ka dauki wannan mataki, sun mori ilmin boko kyauta ne a lokacinsu. Bai kamata ya zama karatu sai ‘dan gidan wane da wane ba.”

Kungiyar ta jawo hadisan Annabi (SAW), ta yi kira ga Nasiru El-Rufai da kwamishinan ilmi, Dr. Muhammad Shehu Usman Makarfi, su duba wannan lamarin.

Kafin nan kun ji cewa kungiyar malaman jami'a ta ASUU ta ce karin 500% a kan kudin karatu zai sa dole wasu yara su hakura da Makarantu da jami'o'in Kaduna.

Shugaban ASUU na KASU ya ce a dalibai za su canza wurin karatu saboda ba su da hali. Peter Adams ya ce iyayen yara ba za su iya biyan wadannan kudin ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel