Da sauran kwana: Allah ya ceci ‘Dan Majalisar Katsina daga hannun wasu ‘Yan bindiga

Da sauran kwana: Allah ya ceci ‘Dan Majalisar Katsina daga hannun wasu ‘Yan bindiga

- ‘Yan bindiga sun nemi su sace Honarabul Jabiru yusufu Yau-Yau a Katsina

- Jabiru yusufu Yau-Yau shi ne mai wakiltar mazabar Batsari a Majalisar jiha

- Wasu sun kyankyasa wa ‘dan siyasar da harin, sai ya bi ta barauniyar hanya

Rahotanni sun bayyana cewa ‘dan majalisa mai wakiltar yankin Batsari, Jabiru yusufu Yau-Yau, ya tsira daga hannun wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne.

Jaridar The Katsina Post ta rahoto cewa Honarabul Jabiru yusufu Yau-Yau ya fada hannun wasu miyagu, amma Ubangiji ya tsaga ya na da sauran kwana.

‘Yan bindigan sun kai wa ‘dan majalisar jihar hari ne a wani kauye da ake kira Garwa, a lokacin da ya kai ziyara domin ya yi wa wasu al’umma ta’aziyya.

KU KARANTA: Ana neman yi wa Gwamnatin Buhari juyin mulki

A ‘yan shekarun bayan nan, ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane sun addabi jihar Katsina.

Rahotanni sun nuna cewa akwai yiwuwar mutanen kauyen ne su ka kai wa ‘yan bindiga labarin zuwan ‘dan majalisan, su kuma su ka shirya tare shi a hanya.

Kamar yadda mu ka samu labari, ‘yan bindigan sun yi gayya ne su na jiran Jabiru yusufu Yau-Yau a kan babura, amma sai ya kaurace wa hanyar da su ka tare.

Wasu Bayin Allah sun kubutar da Jabiru yusufu Yau-Yau, su ka bi da shi ta wani daji, ta haka ne ya yi nasarar kewaye tarkon da miyagun su ka shirya masa.

KU KARANTA: An kashe Kwamishina, an sace Chairman a Kogi

Da sauran kwana: Allah ya ceci ‘Dan Majalisar Katsina daga hannun wasu ‘Yan bindiga
Majalisar Katsina Hoto: www.katsinapost.com.ng
Asali: UGC

‘Dan siyasar ya samu labarin an tare hanyar da ya shigo, don haka ya bi ta barauniyar hanya a jeji.

Wasu jami’an tsaro sun hadu da ‘dan majalisar mai wakiltar mazabar Batsari, inda su ka yi masa rakiya har ya koma garin Katsina ba tare da an auka masa ba.

A au ne ku ka samu labari cewa 'yan bindigan da su ka yi garkuwa da shugaban karamar hukuma a Yagba, jihar Kogi, sun lafta kudin fansar N100m a kansa.

Miyagun ‘Yan bindiga sun tuntubi ‘Yanuwan ‘Chairman’, sun bukaci a turo da kudin fansa. Wani shugaban karamar hukumar ya karbi tattaunawar da ake yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel