Malamai ba su goyon bayan Gwamna El-Rufai ya kara kudin makarantar Jami’ar KASU

Malamai ba su goyon bayan Gwamna El-Rufai ya kara kudin makarantar Jami’ar KASU

- Kungiyar ASUU ta yi tir da matakin da gwamnatin Nasir El-Rufai ta dauka

- Malaman makarantar sun ce karin kudi zai sa dalibai su canza wurin karatu

- Shugaban ASUU, Peter Adams ya ce iyayen yara ba za su iya biyan kudin ba

Malaman jami’ar jihar Kaduna, sun nuna adawar su ga karin kudin karatun da aka yi. Jaridar Daily Trust ta ce malaman sun hakan na tafe da matsala.

Kungiyar ASUU ta malaman jami’a ta ce za a samu raguwar dalibai a makarantar saboda mafi yawan iyayen yaran da ke karatu talakawa ne marasa hali.

ASUU ta reshen jami’ar KASU ta ce iyayen dalibai ba za su iya daukar dawainiyar ‘ya ‘yansu bayan gwamnatin jihar Kaduna ta kara kudin karatun ba.

KU KARANTA: Ba mu kara kudin makaranta ba, amma za mu yi karin - KASU

Malamai ba su goyon bayan Gwamna El-Rufai ya kara kudin makarantar Jami’ar KASU
Jami’ar KASU
Asali: Twitter

Malaman jami’ar sun yi kira ga gwamnatin Nasir El-Rufai da ta janye matakin da ta dauka na yin karin kudi, ta yi abin da ba zai wahalar da marasa karfi ba.

Jami’ar KASU ta na da dalibai 19, 000 wanda 17, 000 daga cikinsu daga jihar Kaduna su ka fito.

Shugaban kungiyar ASUU na reshen jami’ar ta Kaduna, Peter Adamu ya bayyana wannan a jiya. Adamu ya ce 'yan ya-ku-bayi ne duk su ke karatu a KASU.

Peter Adamu yake cewa: “Akalla kashi 70% na yaran gida da ke karatu a makarantar ‘ya ‘yan manoma, ma’aikatan gwamnati da kananan ‘yan kasuwa ne.”

KU KARANTA: Gwamnatin Jihar Kaduna ta kori wasu malamai daga aiki

Abin da ya fi muni shi ne gwamnatin jihar ta kori mutane da yawa daga cikin ma’aikatanta, cikinsu akwai iyaye da masu daukar nauyin dalibanmu.”

“Wadannan mutane su na wahala ne domin su biya kudin makaranta a wannan yanayin tattalin arziki da ake ciki. Karin 500% zai sa dubunnai su bar karatu.”

Adamu ya ce babu hikima a matakin da aka dauka lokacin da ake fama da satar mutane, sannan ya soki tsarin biya wa dalibai kudin karatu da aka shigo da shi.

Kwanakin baya kun ji cewa jami’ar KASU sai yaran su wane-da-wane bayan Gwamnatin NasirEl-Rufai ta yi sabon karin kudi da wasu za su rika biyan N500, 000.

Gwamnatin da ta yi alkawarin ba ‘Dan Talaka karatu ta ribanya kudin karatun Jami’ar. Hukumar makarantar ta bayyana abin da ya sa aka yi wannan kari mai yawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel