Sabon salo: 33% na ‘Yan siyasa sun gagara cin jarrabawar shiga takara a APC a Kaduna

Sabon salo: 33% na ‘Yan siyasa sun gagara cin jarrabawar shiga takara a APC a Kaduna

- ‘Yan siyasa 38 ne ba su yi nasara a jarrabawar da APC ta shirya a Kaduna ba

- Duk mai neman yin takarar shugaban karamar hukuma sai da ya yi jarrabawa

Mutane su na cigaba da tofa albarkacin bakinsu a kan shirin shiga takarar APC domin fitar da gwanin zaben kananan hukumomin jihar Kaduna da aka yi.

Daily Trust ta ce ana surutu ne bayan da mutum 38 da su ke harin kujerar shugabannin kananan hukumomi a karkashin jam’iyyar APC, su ka fadi jarrabawa.

Jaridar ta ce cikin ‘yan siyasa 115 da su ka rubuta jarrabawar da aka shirya wa masu neman tuta a APC, an samu mutane 38 da ba su yi abin kirki a jarrabawar ba.

KU KARANTA: Buhari ya yi wa matasa albashir a kan shirin N-Power

Duk da an samu 33% da ba su samu nasara a jabbawar nan ba, akwai mutane 75 da su ka tabuka abin kwarai, hakan ya ba su damar shiga zaben fitar da gwani.

Daya daga cikin wadanda su ka fadi jarrabawar, Mohammed Sani Abdulmajid, wanda aka fi sani da MS Ustaz ya soki wannan sabon tsari da aka kawo a Kaduna.

A cewarsa, ya samu 52.8%, amma aka ce bai isa shiga takarar ba, a daidai wannan lokaci an kyale wadanda ya fi kokari shiga takarar a wasu kananan hukumomi.

Tuni dai Mohammed Sani Abdulmajid ya rubuta wa kwamitin da ke da alhakin sauraron korafi da takardarsa, ya na kalubalantar hana sa shiga takarar da aka yi.

KU KARANTA: Ganduje ya karawa malamai shekarun ritaya, daga 60 zuwa 65

Sabon salo: 33% na ‘Yan siyasa sun gagara cin jarrabawar shiga takarar APC a Kaduna
Masu son shiga takara a APC su na jarrabawa
Asali: Twitter

Amma jam’iyyar APC ta reshen jihar Kaduna, ta bakin mai magana da yawunta, Salisu Tanko Wosono, ta bayyana cewa ba ta san wani wanda ya shigar da kara ba.

Haka zalika wani daga cikin wadanda su ka rubuta jarrabawar, Musa Dan’azumi ta hannun Lawal Chanchangi, ya ce ba su yarda da wannan sakamakon da aka fitar ba.

Shi kuwa Ibrahim Ismail mai neman tutar takarar kujerar shugaban karamar hukumar Kaduna ta Kudu, ya ji dadin yadda jarrabawar ta kasance bayan ya yi nasara.

A baya kun ji cewa Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe ya yi kira ga shugaban kasa da Gwamnoni lokacin da ya ke darashin azumin Ramadan a garin Kaduna.

A wajen darashin tafsirin da yake gabatar wa, Kabiru Haruna Gombe, ya yi kira ga shugaban Najeriya ya buda baitul-malin gwamnati domin a saya wa talaka wa abinci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel