Tsaro: Matasan Tibi Sun Buƙaci Ortom Ya Haɗa Kai da Buhari

Tsaro: Matasan Tibi Sun Buƙaci Ortom Ya Haɗa Kai da Buhari

- Kungiyar matasan Tiv sun bukaci hadin gwiwa tsakanin gwamnatin Benue da ta Tarayya don magance matsalar tsaro a jihar

- Tyohemba Denen, shugaban kungiyar matasan Tiv ya ce bai kamata a siyasantar da rayuwakan mutane ba

- Kungiyar ta roki gwamnati da jami'an tsaro da su samar da mafita ta dindindin don kawo karashen matsalar

Wata kungiyar matasa, Tiv Youth Advancement Vanguard (TYAV), tayi kira ga gwamnan Jihar Benue, Samuel Ortom, da ya hada kai da gwamnatin tarayya da samar da mafita ga matsalar tsaron jihar maimakon zarge-zarge.

Shugaban kungiyar, Barista Tyohemba Denen a wani taron manema labarai da ya gudana a Abuja ranar Litinin, ya shaida cewa lokacin da kashe mutane da sauran ayyukan ta'addanci suka zama abun bakin ciki a jihar, kamata ya yi gwamnatin jihar da ta tarayya su hada kai don samar da mafita maimakon zargi ko sanya siyasa a rayuwar mutane.

DUBA WANNAN: An Kama Soja da Harsashi Sama da 2000 a Tashar Mota a Maiduguri

Tsaro: Matasan Tibi Sun Buƙaci Ortom Ya Haɗa Kai da Buhari
Tsaro: Matasan Tibi Sun Buƙaci Ortom Ya Haɗa Kai da Buhari. Hoto: Fadar Shugaban Kasa
Asali: Twitter

"Rashin tsaro a Jihar Benue ba laifin mutum ko kungiya daya bane. Matsalar tsaron Sankera, Konshisha da sauran wurare ba ruwan su da Fulani.

"Duba da yadda gwamnan yafi maida hankali kan sha'anin Fulani yana banzatar da rashin tsaron da ke wadannan wurare ya nuna cewa yafi sha'awar siyasa fiye da magance matsalar a yadda take.

"Ko da yaushe ana kashe kashe a Sankera da ya hada da kananan hukumomi uku na Ukum, Logo da Katsina-Ala wadda ya janyo rasuwar rayuwaka da dama ba tare da gwamnan yana ambaton su ba.

"A baya bayan nan, an sace wasu sojoji, aka kashe tare da kona sojoji sha biyu wanda ke aikin samar da zaman lafiya a iyakar Konshisha da karamar hukumar Oju. Wannan mummunan hadari ya janyo lalacewar dukiya ba tare da gwamnan ya dauki wani kwakwarran mataki ba.

"A Tyo-Mu inda gwamnan yayi ikirarin cewa Fulani sun mamaye, akwai rikicin fili tsakanin Hyarev da Kparev tsawon shekaru.

KU KARANTA: Da Ɗuminsa: An Damƙe Wanda Ake Zargi da Ɗaukan Nauyin Kai Hare-Hare a Imo

"Karuwar kashe kashe da yan kungiyar asiri na bukatar hadin kai tsakanin gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro don dakile karuwar ta'addanci a jihar," a cewar kungiyar.

Kungiyar ta ce yadda gwamnan da masu masu magana da yawun shugaban kasa ke yi dangane da batun abin takaici duba da yadda rashin tsaro ya addabi jihar tare da rokon gwamanti da jami'an tsaro da su zage damtse wajen samar da mafita ta dindindin ga matsalar.

A wani labarin daban kunji wasu matasa a Daura, a ranar Alhamis 29 ga watan Afrilu sun kaddamar da kungiyar ta goyon bayan Dr Abubakar Bukola Saraki ya fito takarar shugabancin kasa a zaben 2023, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban kungiyar, Abubakar Nuhu Adam, ya ce sun yanke shawarar kafa kungiyar na goyon bayan tsohon shugaban majalisar ya yi takarar shugaban kasa ne saboda abin da ya yi da kuma abubuwan da ya ke yi wa matasa a kasar.

Hon. Adam ya bada misali dokar 'Not Too Young To Run' da aka aiwatar lokacin Saraki na shugabancin majalisa da kuma goyon bayan da ya bawa matasa su yi takarar kwamitin zartawar na jam'iyyar PDP da wasu sauransu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel