Yan Boko Haram sun hallaka Malamai uku a garin Geidam, jihar Yobe

Yan Boko Haram sun hallaka Malamai uku a garin Geidam, jihar Yobe

- An kashe malaman makaranta uku a jihar Yobe makon da ya gabata

- Wannan ya auku ne lokacin da yan Boko Haram suka kai hari Geidam

- Mutan garin Geidam sun gudu daga muhallansu bayan harin da yan ta'addan suka kai

Yan ta'addan Boko Haram da suka kai hari karamar hukumar Geidam, a jihar Yobe, makon da ya gabata sun hallaka akalla Malaman makaranta uku.

A cewar Daily Trust, an kashe biyu cikin Malaman a makarantar Government Technical School, Geidam, yayinda aka kashe daya a gida.

Yan ta'adda sun yi kokarin jan hankulan matasa domin su shiga tafiyarsu.

Sun bankawa gidajen ma'aikatan gwamnati da yan siyasa wuta bayan kwashe kayayyakin alfanu.

Mutan garin sun bayyana cewa ba zasu taba manta abubuwan da suka faru cikin kwanaki biyar da yan Boko Haram suka kwace garin ba.

DUBA NAN: Hada baki da yan bindiga: Sarkin Katsina ya dakatad da Hakimin Kankara

Yan Boko Haram sun hallaka Malamai uku a garin Geidam, jihar Yobe
Yan Boko Haram sun hallaka Malamai uku a garin Geidam, jihar Yobe
Asali: UGC

KU KARANTA: A jihar Kano kadai ake yaki da rashawa kamar EFCC da ICPC, Gwamna Ganduje

Hakazalika, yan ta'addan sun rabawa mazauna garin Geidam a jihar Yobe kudi domin shigar da su cikin harkar ta'addancin da suke yi.

HumAngle ta samu rahoton cewa yan ta'addan sun yi rabon N20,000 ga kowane gida ga gidaje akalla 50 da yammacin Talata.

Yan ta'addan sun kai hari karamar hukumar ne da yammacin Juma'a, 23 ga Afrilu, kuma suka kwace garin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel