Hada baki da yan bindiga: Sarkin Katsina ya dakatad da Hakimin Kankara

Hada baki da yan bindiga: Sarkin Katsina ya dakatad da Hakimin Kankara

- Ana zargin wani Sarkin gargajiya da goyawa yan bindiga baya a garin Katsina

- Wannan ya biyo bayan mutuwan dan bindigan da ya sace dalibai a Kankara

- An dakatad da Hakimin har sai bayan an kammala bincike kansa

Masarautar Katsina ta dakatad da da Hakimin Garin Kankara, Abubakar Yusuf, kan zargin hada baki da yan bindiga da suka addabi al'ummarsa.

Kakakin majalisar Sarki, Iro Bindawa, a ranar Asabar ya bayyana cewa an dakatad da Hakimin ne bisa korafe-korafen mazauna gari da kuma binciken jami'an tsaro.

Kakakin ya kara da cewa an dakatad da shi ne domin taimakawa gwamnati wajen kawo karshen ayyukan yan bindiga.

Majalisar ta kaddamar da kwamiti don binciken Hakimin bisa zarge-zargen da ake masa na taimakawa yan bindigan da suka addabi jama'arsa.

Ire-iren haka suna faru a jihar Katsina inda akayi zargin Sarakunan gargajiya da hada kai da yan bindiga wajen cutar da al'ummarsu.

A kwanakin baya, gwamnan jihar Zamfara ya kwancewa Sarkin Maru rawani.

KU KARANTA: Shirin Dadin Kowa a Ramadan: Iyaye sun yi kira ga a canza lokacin shirin

Hada baki da yan bindiga: Sarkin Katsina ya dakatad da Hakimin Kankara
Hada baki da yan bindiga: Sarkin Katsina ya dakatad da Hakimin Kankara
Asali: Twitter

KU KARANTA: A jihar Kano kadai ake yaki da rashawa kamar EFCC da ICPC, Gwamna Ganduje

A bangare guda, an kashe hatsabibin dan bingida Auwalu Daudawa da aka fi sani da sace dalibai fiye da 300 daga makarantarsu da ke Kankara a jihar Katsina.

Daily Trust ta ruwaito cewa an bindige shi yayin fada tsakaninsa da wasu kungiyar yan bindigan a yammacin ranar Juma'a a dajin Dumburum da ke tsakanin karamar hukumar Zurmi a Zamfara da Batsari a jihar Katsina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel