A jihar Kano kadai ake yaki da rashawa kamar EFCC da ICPC, Gwamna Ganduje

A jihar Kano kadai ake yaki da rashawa kamar EFCC da ICPC, Gwamna Ganduje

- Gwamna Ganduje ya yi alfahari da hukumar korafe-korafe da yaki da rashawan jihar

- Gwamnan ya ce babu irin hukumar a jihohin Najeriya

- Ya jinjinawa shugaban hukumar Muhuyi Rimingado bisa kokarin da yake yi

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a ranar Alhamis ya bayyana cewa a jihar Kano kadai ake yaki da cin hanci da rashawa kamar yadda gwamnatin tarayya ke yi.

Ganduje ya bayyana hakan ne yayin rantsar da kwamitin tafiyar da dabarun yaki da rashawa na hukumar korafe-korafe da yaki da rashawan jihar Kano.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Usman Alhaji, ya ce wannan ce kwamiti mafi muhimmanci da za'a rantsar kan yaki da rashawa.

"A jihar Kano kadai ake yaki da rashawa kamar yadda akeyi a gwamnatin tarayya. Ina mai tuna cewa kwamishanoni biyu da sakatarorin din-din-din sun rashawa kujerunsu sakamakon ayyukan hukumar yaki da rashawa," Ganduje yace.

"Hakan na nufin cewa babu wanda ya fi karfin a hukuntashi idan aka kamashi da kashia gindi. Hakan na nufin cewa hukumar na aiki. Ko ku yarda, ko kada ku yarda, rashawa na kashe mu."

Ganduje ya jinjinawa ayyukan shugaban hukumar, Muhuyi Rimingado, wajen dakile cin hanci da rashawa.

KU KARANTA: Shirin Dadin Kowa a Ramadan: Iyaye sun yi kira ga a canza lokacin shirin

A jihar Kano kadai ake yaki da rashawa kamar EFCC da ICPC, Gwamna Ganduje
A jihar Kano kadai ake yaki da rashawa kamar EFCC da ICPC, Gwamna Ganduje
Asali: Facebook

DUBA NAN: Hada baki da yan bindiga: Sarkin Katsina ya dakatad da Hakimin Kankara

A bangare guda, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa cin hanci da rashawa ba zai bari a samu cigaba na kwarai a Najeriya ba.

A cewar Ganduje, da irin wannan cin hanci da rashawar da akeyi a Najeriya, da kamar wuya a samu cigaba saboda cin hanci yana kashe kasar.

Ya bayyana hakan ne a zaman kaddamar da wani kwamiti na musamman na dabarun yaki da rashawa a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng