Yan Boko Haram sun fara rabawa mutane N20,000 a garin Geidam

Yan Boko Haram sun fara rabawa mutane N20,000 a garin Geidam

Yan ta'addan Boko Haram (ISWAP) sun fara rabawa mazauna garin Geidam a jihar Yobe kudi domin shigar da su cikin harkar ta'addancin da suke yi.

HumAngle ta samu rahoton cewa yan ta'addan sun yi rabon N20,000 ga kowane gida ga gidaje akalla 50 da yammacin Talata.

Yan ta'addan sun kai hari karamar hukumar ne da yammacin Juma'a, 23 ga Afrilu, kuma suka kwace garin.

Yan ta'addan sun lalata dukiyoyin gwamnati da na jama'a masu zaman kansu , wanda ya hada da dukiyoyin kamfanonin sadarwa, amma basu cutar da fararen hula ba musamman Musulmai.

Hakazalika sun daga tutarsu a garin domin gayyatar mutane da su shiga kungiyar.

Yan Boko Haram sun fara rabawa mutane N20,000 a garin Geidam
Yan Boko Haram sun fara rabawa mutane N20,000 a garin Geidam
Asali: UGC

Wani dan majalisar wakilai, Lawan Shettima ya bayyana cewa karya hukumar Soji sukeyi cewa sun ragargaji yan ta'addan ranar Lahadi.

"Mutanenmu na cikin wani hali, ta yaya a matsayin mutum na dan Najeriya amma Boko Haram ke mulkin garin tsawon awanni 24 kuma kamar babu ruwan kowa," yace.

Mutanen Geidam da dama sun gudu daga garin.

Daya daga cikinsu, Rawana Usman, ya bayyanawa Daily Trust cewa yan ta'addan sun kashe Kiristoci biyu ma'aikatan kungiyoyin agaji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel