Jerry Gana Ya Yi Barazanar Maka Majalisar Ƙolin Musuluncin Nigeria a Kotu

Jerry Gana Ya Yi Barazanar Maka Majalisar Ƙolin Musuluncin Nigeria a Kotu

- Tsohon ministan sadatwa Jerry Gana na ya bukaci majalisar kolin addinin musulunci da ta janye kalamanta a kansa

- Gana ta bakin lauyansa ya ce ba shi da alaka ta kusa ko nesa da Muhammad Yusuf wanda wanda ya kafa Boko Haram

- Tsohon ministan ya ce muddin majalisar kolin musuluncin bata janye maganar ba zai maka ta a gaban kuliya

Jerry Gana, tsohon ministan sadarwar, ya bukaci majalisar kolin harkokin addinin musulunci (NSCIA) da ta janye kalamanta da suka alakanta shi da Mohammed Yusuf, wanda ya fara kafa Boko Haram, rahoton The Cable.

NSCIA, yayin da take kare Isa Pantami, ministan sadarwa, wanda ke fuskantar matsin lamba saboda ya taba goyon bayan wasu kungoyoyin ta'addanci, sun yu ikirarin cewa akwai wani kirista wanda yake minista ne a lokacin, ya yi belin Muhammad Yusuf har sau uku a 2008.

Ban san shugaban Boko Haram ba, Jerry Gana ya bukaci NSCIA ta janye kalamanta
Ban san shugaban Boko Haram ba, Jerry Gana ya bukaci NSCIA ta janye kalamanta. Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An Harbe Auwalu Daudawa Har Lahira Kwana Huɗu Bayan Komawarsa Daji

Duk da NSCIA bata ambaci sunan ministan ba, Jeo-Kyari Gadzama mai lambar (SAN) kuma lauyan gana, a wata takarda da ya aike wa NSCIA mai kwanan watan 29 ga april, 2021, yace mutane sun san da wanda yake karewa ake.

Ya tabbatar da cewa Gana bashi da alaka da wanda ya kafa Boko Haram din.

"Muna sanarwa, a madadin wanda muke wakilta, sabanin rahoton karya da aka yada, wanda muke karewa bai taba, ta kowacce irin fuska yin belin Malam Muhamad Yusuf ba" kamar yadda sanarwar ta ce.

"Wanda muke karewa bashi da alaka, ta kusa ko ta nesa da Yusuf, kuma basu taba zama tare ba, ba abokai bane, kuma baya goyon bayan Boko Haram kamar yadda NSCIA tayi zargi."

KU KARANTA: Abba Swags: An Cafke Matashin da Ya Sace Wayoyin Naira Miliyan 15 a Katsina

Lauyan ya kara da cewa kamar yadda kuka sani lamarin ya yi nisa a kafafen sadarwa na zamani har ma ya zama abun tattaunawa tsakanin mutane, yasa akwai bukatar sanar da mutane Gana ba dan Ta'adda bane.

Ya kuma bukaci da NSCIA da ta janye kalamanta ko kuma su dauki matakin Shariah

A wani labarin daban kunji wasu matasa a Daura, a ranar Alhamis 29 ga watan Afrilu sun kaddamar da kungiyar ta goyon bayan Dr Abubakar Bukola Saraki ya fito takarar shugabancin kasa a zaben 2023, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban kungiyar, Abubakar Nuhu Adam, ya ce sun yanke shawarar kafa kungiyar na goyon bayan tsohon shugaban majalisar ya yi takarar shugaban kasa ne saboda abin da ya yi da kuma abubuwan da ya ke yi wa matasa a kasar.

Hon. Adam ya bada misali dokar 'Not Too Young To Run' da aka aiwatar lokacin Saraki na shugabancin majalisa da kuma goyon bayan da ya bawa matasa su yi takarar kwamitin zartawar na jam'iyyar PDP da wasu sauransu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel