Da duminsa: Yan bindiga sun kai hari makarantar Boko a Plateau, sun kwashe dalibai 2

Da duminsa: Yan bindiga sun kai hari makarantar Boko a Plateau, sun kwashe dalibai 2

- A yau kuma, wasu yan bindiga dadi sun yi kokarin kwashe daliban makaranta a Najeriya

- Wannan karon a jihar Pleteau, Arewa maso tsakiyar Najeriya aka kai hari

- Jami'an tsaron dake wajen sun dakile yunkurin yan bindigan kuma hakan ya ceci rayukan daliban

Yan bindiga sun yi awon gaba da daliban makarantar Mission ta Calvary International Ministry, CAPRO, dake karamar hukumar Barkin Ladi, a jihar Plateau.

Makarantar na kusa da tashar jirgin saman kasa da kasa ta Yakubu Gowon a jihar.

Masu idon shaida sun bayyana cewa yan bindigan sun dira makarantar ne da daren Laraba, 28 ga Afrilu.

Wani ganau ya bayyanawa TheNation cewa yan bindigan sun yi kokarin sace dimbin dalibai dake bacci amma daliban suka ankara da wuri suka kira jami'an tsaro.

Ba tare da bata lokaci ba jami'an tsaron suka bude musu wuta, amma sun samu nasaran tafiya da dalibai biyu.

Daga baya daya daga cikin dalibai ya samu guduwa yayinda akayi musayar wuta tsakanin yan bindiga da jami'an tsaro.

Hukumar makarantar bata saki jawabi kan abinda ya faru ba tukun amma kakakin yan sandan jihar, ASP Gabriel Ubah, ya tabbatar da labarin.

DUBA NAN: Jerin kasashe 20 mafi rashin shugabancin kwarai a duniya, Rahoton Bincike

Da duminsa: Yan bindiga sun kai hari makarantar Boko a Plateau, sun kwashe dalibai 2
Da duminsa: Yan bindiga sun kai hari makarantar Boko a Plateau, sun kwashe dalibai 2
Asali: UGC

KU DUBA: Babu cigaban da za'a samu a Najeriya muddin ana irin wannan cin hanci da rashawan, Ganduje

A bangare guda, an tsaurara matakan tsaro a zauren majalisar ƙasar nan saboda jami'an tsaro na ɗaukar dogon lokaci suna bincikar abubuwan hawan dake ƙoƙarin shiga harabar zauren.

Daga gudanar da Wa'azi Binciken abubuwan hawa a yau ya zarta na kowanne rana wanda hakan ya haddasa dogon layi a hanyar shiga zauren majalisar, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel