Babu cigaban da za'a samu a Najeriya muddin ana irin wannan cin hanci da rashawan, Ganduje

Babu cigaban da za'a samu a Najeriya muddin ana irin wannan cin hanci da rashawan, Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa cin hanci da rashawa ba zai bari a samu cigaba na kwarai a Najeriya ba.

A cewar Ganduje, da irin wannan cin hanci da rashawar da akeyi a Najeriya, da kamar wuya a samu cigaba saboda cin hanci yana kashe kasar.

Ya bayyana hakan ne a zaman kaddamar da wani kwamiti na musamman na dabarun yaki da rashawa a jihar, rahoton BBC Hausa.

"Za ku yarda da ni idan na ce cin hanci yana kashe mu. Maganar gaskiya ita ce ba inda kasar za ta je da wannan cin hanci. Ba za mu motsa ko ina ba," in ji Ganduje.

An kaddamar da wannan kwamitin ne a ranar Alhamis, 29 ga watan Afrlu, 2021.

Babu cigaban da za'a samu a Najeriya muddin ana irin wannan cin hanci da rashawan, Ganduje
Babu cigaban da za'a samu a Najeriya muddin ana irin wannan cin hanci da rashawan, Ganduje Hoto: Salihu Tanko Yakassai
Asali: Twitter

Asali: Legit.ng

Online view pixel