Jerin kasashe 20 mafi rashin shugabancin kwarai a duniya, Rahoton Bincike

Jerin kasashe 20 mafi rashin shugabancin kwarai a duniya, Rahoton Bincike

- Wata kungiyar shugabancin kwarai ta saki rahoto da ya nuna jerin kasashen duniya mafi rashin shugabannin kwarai a duniya

- A rahoto da kungiyar CGGI ta saki, kasar Venezeula ce kasa ta karshe cikin masu shugabannin kwarai a duniya

- Kasar Zimbabwe ce ta biyu sannan kuma kasar Najeriya ta uku

Wata kungiya mai zaman kanta a kasar Singapore, Chandler Good Government Index, CGGI ta bayyana jerin kasashen da suka fi shugabannin kwarai a fadin duniya.

Rahoton da aka saki ranar 26 ga Afrilu, ya bayyana cewa an yi amfani da karfin iya yaki da rashawa wajen nuna irin nagartan shugabannin kasa.

CGGI ta saki rahotonta a shafinta na Tuwita.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Diraktan CGGI, Wu Wei Neng, ya ce mulki na kwarai ne abinda zai iya kawo wa kasa nasara.

An bada maki ga kowace kasa ne bisa abubuwa guda 7: Nagartan shugabannin da hangen nesa, dokokin kwarai, ma'aikatu na kwarai, gaskiya da rashin cin amana, janyo hankalin masu sa hannun jari.

Sauran sune mutuncin kasar a idon duniya, da kuma taimakon marasa karfi da tayar da su daga makaskancin hali.

Ga jerin kasashen:

1. Kasar Venezuela

2. Kasar Zimbabwe

3. Kasar Najeriya

4. Kasar Mozambique

5. Kasar Mali

6. Kasar Iran

7. Kasar Madagascar

8. Kasar Lebanon

9. Kasar Burkina Faso

10. Kasar Zambiya

KU KARANTA: Jerin kasashe 20 mafi shugabannin kwarai a duniya, Rahoton Bincike

11. Kasar Aljeriya

12. Kasar Habasha (Ethiopia)

13. Kasar Nepal

14. Kasar Pakistan

14. Kasar Malawi

16. Kasar Nicaragua

17. Kasar Guatemala

18. Kasar Ecuador

19. Kasar Cambodia

20. Kasar Tajikistan

Jerin kasashe 20 mafi rashin shugabannin kwarai a duniya, Rahoton Bincike
Jerin kasashe 20 mafi rashin shugabannin kwarai a duniya, Rahoton Bincike Hoto: @ChandlerINST
Asali: Twitter

Shiga nan don karanta cikakken rahoto

A bangare guda, wani dan majalisar tarayya a ranar Alhamis ya ce Majalisar Dokoki ta kasa za ta bijiro da batun tsige Shugaba Muhammadu Buhari idan bangaren zartarwa ba ta yi aiki da kudurin ta na tsaro ba.

Majalisar wakilai a ranar Laraba ta kaddamar da wani kwamiti na mutune 40 don samar da mafita ga kalubalen tsaron kasar.

Kwamitin zai shirya taron kwanaki hudu na tsaro a watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel