Hadiman ‘Yan Majalisa sun yi zanga-zanga a kan shafe watanni 22 ba a biya su kudinsu ba

Hadiman ‘Yan Majalisa sun yi zanga-zanga a kan shafe watanni 22 ba a biya su kudinsu ba

- Hadiman ‘Yan Majalisa sun kuma yin zanga-zanga a tsakiyar makon nan

- Mukarraban da ke Majalisa sun ce an hana su hakkokinsu na shekara biyu

- Wannan ne karo na biyu da aka yi zanga-zangar a Majalisa a watan Afrilu

Rahotanni sun tabbatar mana da cewa Mukarraban ‘yan majalisar tarayya sun sake shirya wata zanga-zanga a ranar Laraba, 28 ga watan Afrilu, 2021.

Masu aikin taimaka wa da bada shawara a majalisar sun gudanar da zanga-zanga a harabar majalisar ne a dalilin wasu hakkokansu da su ka makale.

Premium Times ta ce hadiman da ke aiki a majalisar su na bin bashin albashin har watanni 22.

‘Yan jarida sun ga wadannan ma’aikata a harabar majalisar dauke da takardu, su na kiran shugabannin majalisa su biya su kudin da su ke bi bashi.

KU KARANTA: Hukumar Majalisa ta nada Ojo Amos Olatunde a matsayin magatakarda

Masu wannan zanga-zanga su na zargin shugabannin ma’aikatan majalisar da kin dabbaka sabon tsarin albashin rukuninsu na CONLESS da aka kawo.

Haka zalika mukarraban ‘yan majalisar Najeriyar sun ce an gagara fara biyansu sabon mafi karancin albashi, kuma an cinye masu alawus din zirga-zirga.

Zebis Prince ya yi wa manema labarai magana a madadin sauran abokan aikinsa, ya ce an hana su hakkokinsu duk da majalisa ta na da wadannan kudi a kasa.

Ya ce: “Makonni biyu da su ka wuce, mu na nan, mun yi zanga-zanga a kan bashin albashinmu.”

KU KARANTA: Tsofaffin Ministoci, Sanatoci, Gwamnoni sun saye gidajen Biliyoyi a Dubai

Hadiman ‘Yan Majalisa sun yi zanga-zanga a kan shafe watanni 22 ba a biya su kudinsu ba
Majalisar Tarayya
Asali: Twitter

“Abin takaici da bakin ciki ne makonni biyu bayan mun yi wa shugaban majalisa, Femi Gbajabiamila, magana, ya ce ba a kyauta ba, an ki yin komai a kai."

Prince ya zargi shugabannin majalisar da salwantar da kudi har N9.6bn. “Mu na da labari an ware wannan kudi, amma abin takaici yanzu ana cewa babu kudin nan.”

Wannan ne karo na biyu a cikin ‘yan makonnin nan da hadiman ‘yan majalisar su ka yi irin wannan zanga-zanga a kan a biya su alawus din aikin da su ka yi.

A tsakiyar watan Afrilu nan, ma’aikatan sun yi irin wannan zanga-zanga, inda su ka zargi akawun majalisa, Ojo Olatunde, da kin biyansu wasu tulin hakkoki.

Wadannan mukarrabai sun zargi Ojo Olatunde da lakume bashin albashin aikin da su ka yi tun 2019.

Asali: Legit.ng

Online view pixel