Yanzu-Yanzu: Ma'aikatan Majalisa Sun Janye Yakin Aikin Suka Yi Barazanar Shiga

Yanzu-Yanzu: Ma'aikatan Majalisa Sun Janye Yakin Aikin Suka Yi Barazanar Shiga

- Ma'aikatan majalisar tarayya sun fasa zuwa yajin aikin da suka yi barazanar yi

- Hakan na zuwa ne bayan an sassanta tsakaninsu da mahukunta an rattaba hannu kan yarjejeniya

- Yarjejeniyar ta kunshi bukatunsu da suka hada da biyan allawus, sabon albashi da sauransu

Mahukunta a Majalisar Tarayya da ma'aikatan majalisar sun sassanta rashin jituwan da ke tsakaninsu a ranar Talata 13 ga watan Afrilun 2021.

Ma'aitakan karkashin kungiyar su ta ma'aikatar majalisa ta Nigeria sun yi barazanar fara yajin aiki tare da bada wa'adi.

DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Arapaja ya zama sabon shugaban PDP na Kudu maso Yamma

Yanzu-Yanzu: Ma'aikatan Majalisa Sun Janye Yakin Aikin Suka Yi Barazanar Shiga
Yanzu-Yanzu: Ma'aikatan Majalisa Sun Janye Yakin Aikin Suka Yi Barazanar Shiga
Asali: Original

Sun bukaci magatakardar majalisar ta tarayya, Olatunde Ojo ya biya musu bukatunsu idan ba haka ba su shiga yajin aiki.

Amma, mahukunta a majalisar sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da ma'aikatan a ranar Talata inda suka amince za su biya musu dukkan bukatunsu illa guda daya.

KU KARANTA: Ahmed Musa ya ce zai koma buga wa ƙungiyar Kano Pillars wasa

Rattaba hannun ya saka m'aikatan sun janye yajin aikinsu da rufe majalisar da suka yi shirin yi daga ranar Laraba 14 ga watan Afirilu.

Yarjejeniyar ta kunshi abubuwa da dama da ma'aikatan ke neman da kuma lokutan da za a aiwatar da su.

Abubuwan da ke cikin yarejeniyar sun hada da biyan ariyas na albashi mafi karanci daga Mayun 2021 da wasu allawus din.

Kudaden zuwa hutu da za a fara biya daga 19 ga watan Afrilu da kuma kudin hatsarin da ke tattare da aiki wanda za a fara biya daga Yulin 2020 zuwa Afrilun 2021.

Har wa yau akwai batun tagomashi na kudaden biyan gidan haya da sauransu.

Elder Felix Orumwense, Mr Sani Magaji Tambuwal, Mr. Abiodun Suraju Oladoyin, Bassey Etuk, Sunday Sabiyi, Ojemeri Oisamaye ne suka saka hannu kan yarjejeniyar.

A bangare guda kun ji cewa gwamnatin Jihar Kano ta rage albashin masu rike da mukaman siyasa a jihar da kashi 50 cikin 10 na watan Maris saboda karancin kudade, Vanguard ta ruwaito.

Kwamishinan labarai na jihar, Muhammad Garba, ne ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Talata inda ya ce hakan ya faru ne saboda kudin da jihar ke samu daga gwamnatin tarayya a ragu.

Kwamishinan ya ce matakin ta shafi gwamna, mataimakinsa da dukkan masu rike da mukaman siyasa a jihar da suka hada da kwamishinoni, masu bada shawara na musamman, manyan masu taimakawa da masu taimakawa na musamman da sauransu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel