Asiri ya tonu: Tsofaffin Gwamnoni, Ministoci da Sanatoci sun mallaki kadarori 800 a Dubai, Landan

Asiri ya tonu: Tsofaffin Gwamnoni, Ministoci da Sanatoci sun mallaki kadarori 800 a Dubai, Landan

- Manyan ‘Yan kasuwa da ‘Yan siyasan kasar nan sun mallaki kadarori a waje

- Mathew T. Page ya fasa kwan wadanda su ka saye gidaje a Dubai da Landan

- A cikin jerin akwai Gwamnoni, tsofaffin masu mulki, da kasurguman Attajirai

The Nation ta futar da rahoto cewa akwai manya da ‘yan siyasa da su ka rike ofis a Najeriya da ake zargin su na da kadarori a biranen Landan da Dubai.

Tsofaffi da gwamnoni masu-ci 35 da mutane 299 da su ka taba samun mukami ake zargin sun kashe Dala miliyan 400 wajen mallakar kadarori a Dubai.

Cikin wadanda ake zargi da tara dukiya a ketare akwai wani tsohon gwamnan Arewa, tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, da shugaban PDP.

KU KARANTA: Gwamnatin da ta yi alkawarin ba Talaka ilmi ta ribanya kudin karatu a Kaduna

Rahoton ya bayyana cewa akwai tsofaffin Ministoci 15, Alkali daya, ‘yan sanda 14, hafsoshin sojoji, ‘yan majalisa da ma’aikatan NNPC 15 a cikin wannan jerin.

Daga cikin wadanda su ke tara kadarori a kasar wajen akwai tsofaffin shugabannin hukumomin gwamnati 16 da wasu ma’aikatan fadar shugaban kasa 11.

Har ila yau, wannan jeri ya na dauke da manyan ‘yan kasuwa 50 da su ke boye da kudin ‘yan siyasa.

Wani jami’i da ke aiki a cibiyar Chatham House, Mathew Page ya bankado duk wannan a ranar Talata lokacin da yake gabatar da takarda gaban hukumar ICPC.

KU KARANTA: Boko Haram: Jami’an Gwamnati ne su ke saida Sojoji - Dikwa

Asiri ya tonu: Tsofaffin Gwamnoni, Ministoci da Sanatoci sun mallaki kadarori 800 a Dubai, Landan
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Da yake yi wa jami’an ICPC bayani, Mathew Page ya ce ‘yan Najeriya su na fake wa da sunan biyan kudin makaranta da kadarori wajen karakatar da biliyoyi.

Kasashen da aka fi kai kudi daga Najeriya su ne: UAE, Ingila da kuma Amurka. Page ya ce ‘yan Najeriya su na jin dadin hulda da Dubai ne saboda rashin takura.

Yanzu haka akwai gwamnan Arewa mai-ci wanda yake da kadarori takwas na $5m a Dubai, sannan wani shugaban PDP ya saye gidaje 13 a Dubai da Landan.

A jiya ku ka ji mawakin nan Martin Okwun, wanda aka fi sani da J. Martins, ya roki afuwar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan kan abin da aka yi masa.

J. Martins ya ce tsohon shugaban kasar Najeriya ya jure caccaka da kalubale, tare da zagin da jama'a suka rika yi masa, sai ga shi a lokacin APC, ba a ga sauyi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng