Da Dumi-Dumi: Ƴan Bindiga Sun Bankawa Ofishin Ƴan Sanda Wuta a Anambra

Da Dumi-Dumi: Ƴan Bindiga Sun Bankawa Ofishin Ƴan Sanda Wuta a Anambra

- Wasu yan bindiga da ba su san ko su wanene ba sun kai hari caji ofis na yan sanda a jihar Anambra

- Yan sandan sun kona gine-ginen da ke ofishin da babura da motocci na wadanda ake zargi da laifi

- Har wa yau, yan bindigan sun saki mutanen da ake tsare da su a bayan kanta cikin caji ofis din na garin Nkporo

Yan bindiga sun kai hari ofishin rundunar yan sanda ke Nkporo a karamar hukumar Ohafia ta jihar Abia, The Nation ta ruwaito.

Maharan sun kona babban ginin cijin caji ofis na yan sandan.

DUBA WANNAN: Malaman Addinin Kirista Sunyi Tattaki Na Goyon Bayan Pantami a Abuja

Da Dumi-Dumi: Ƴan Bindiga Sun Bankawa Ofishin Ƴan Sanda Wuta a Anambra
Da Dumi-Dumi: Ƴan Bindiga Sun Bankawa Ofishin Ƴan Sanda Wuta a Anambra
Source: Original

Sun kuma kona kayayyakin da yan sandan suka kwace daga hannun wadanda ake zargi da laifi da suka hada da motocci da babura a caji ofis din.

An kuma gano cewa yan bindigan sun saki mutanen da ake tsare da su a bayan kanta yayin harin.

KU KARANTA: Majalisar Ɗinkin Duniya Ta Buƙaci a Saki Mubarak Bala Da Ake Zargi Da Ɓatanci Ga Annabi

Faruwar harin ya jefa mutane da dama a unguwar da yan asalin garin cikin damuwa.

An yi kokarin tuntubar mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Abia, Geoffrey Ogbonna domin ji ta bakinsa amma hakan bai yi wu ba.

Bai daga wayansa ba kuma bai amsa sakon kar ta kwana da aka aika masa ba.

Nkporo ne garin su mataimakin gwamnan jihar Abia, Ude Oko Chukwu.

A wani rahoton daban, Mallam Garba Shehu ya caccaki wadanda suke sukar Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Dr Isa Pantami saboda rashin yafe masa abin da ya yi a baya, Channels Television ta ruwaito.

Ya na ganin rashin yafewa ministan kan maganganun da ya yi na goyon bayan kungiyoyi masu tsatsauran ra'ayi ya fi muni kan laifin da ministan ya aikata.

Babban mai taimakawa shugaban kasar a bangaren watsa labarai ya yi wannan kalaman ne a lokacin da ya bayyana a shirin Politics Today na Channels Television a ranar Juma'a.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel