Malaman Addinin Kirista Sunyi Tattaki Na Goyon Bayan Pantami a Abuja

Malaman Addinin Kirista Sunyi Tattaki Na Goyon Bayan Pantami a Abuja

- Wata kungiyar malaman addinin kirista ta yi tattakin nuna goyon baya ga ministan sadarwa da tattalin arziki na zaman, Dr Isa Ali Pantami

- Bishop Abel King, jagoran masu tattakin ya ce suna goyon bayan matakin da Buhari ya dauka na rashin biyewa masu neman a sauke Pantami

- Malaman addinin kiristan sun ce wasu makiya Nigeria da son zaman lafiya ne ke neman a sauke Pantami saboda aikin da ya ke yi

Kungiyar malaman addinin kirista na 'Forum of Christian Bishops and Clergy Council' ta nuna goyon bayan ta ga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari kan matsayarta game da zargin da ake yi wa ministan Sadarwa da tattalin arziki na zamani, Dr Isa Ali-Pantami.

Kungiyar ta sanar da hakan ne yayin wani tattaki na goyon baya da ta yi a Unity Fountain Abuja, inda ta ce wadanda ke zargin wasu tsirarai ne a kasar da basu son sauye-sauyen da ministan ke yi.

Pantami: Malaman Addinin Kirista Sun Yi Tattaki Na Nuna Goyon Baya a Abuja
Pantami: Malaman Addinin Kirista Sun Yi Tattaki Na Nuna Goyon Baya a Abuja
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: 'Yan Boko Haram Sun Zaƙewa Matan Aure a Niger Bayan Sun Musu Girki Sun Cinye

Malaman addinin na kirista sun fito rike da takardu masu rubutu da ke nuna goyon baya da ga gwamnatin Buhari da rokonsa ya cigaba da hada kan yan kasa.

Har wa yau, kungiyar ta ce ta yi tattakin ne na zaman lafiya domin jadada bukatar zaman lafiya da hadin kai a kasa.

Bishop Abel King, jagoran masu tattakin ya ce ya zama dole su fito su bayyana matsayarsu saboda irin zargin da ake yi wa Mr Pantami.

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: 'Yan Daba Sun Cinnawa Kotun Tarayya Wuta a Ebonyi

"Shugaban kasa bisa hikimarsa ya nuna cewa Nigeria ne ke gabansa kuma zai cigaba da hada kanmu sannan ba zai bari masu son kai su rude shi ba ko tilasta shi," wannan abin yabo ne in ji Bishop Abel.

Bishop Abel ya cigaba da cewa ya kamata mutane su dena la'akari da banbancin addini, kabila ko yanki idan za su dauki mataki sai dai su mayar da hankali kan abin da zai kawo cigaba a kasa.

Kazalika, ya gargadi mutane kan furta kalaman da ka iya tada zaune tsaye a kasar.

A wani rahoton daban, Mallam Garba Shehu ya caccaki wadanda suke sukar Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Dr Isa Pantami saboda rashin yafe masa abin da ya yi a baya, Channels Television ta ruwaito.

Ya na ganin rashin yafewa ministan kan maganganun da ya yi na goyon bayan kungiyoyi masu tsatsauran ra'ayi ya fi muni kan laifin da ministan ya aikata.

Babban mai taimakawa shugaban kasar a bangaren watsa labarai ya yi wannan kalaman ne a lokacin da ya bayyana a shirin Politics Today na Channels Television a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164