Majalisar Ɗinkin Duniya Ta Buƙaci a Saki Mubarak Bala Da Ake Zargi Da Ɓatanci Ga Annabi

Majalisar Ɗinkin Duniya Ta Buƙaci a Saki Mubarak Bala Da Ake Zargi Da Ɓatanci Ga Annabi

- Wata kwamiti kwararru na Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci a saki Mubarak Bala dan asalin jihar Kano da babu ruwansa da addini

- Kwamitin ta yi kira ga mahukunta a kasar su tabbatar an bi umurnin kotun da ta ce a sake shi a biya shi N250,000 na keta hakkinsa

- A cewar kwamitin cigaba da tsare shi bayan kotun ta ce a sake shi take hakkin bil adama ne da keta hakkin yancin walwalwa

Kwamitin kwararru na Majalisar Dinkin Duniya, MDD, ta yi bukaci mahukunta a Nigeria su saki Mubarak Bala, shugaban kungiyar wadanda ba su yin addini a Nigeria da ake tsare da shi kimanin shekara daya, BBC ta ruwaito.

An kama Mubarak tare da tsare shi ne bayan an shigar wa rundunar yan sandan jihar Kano koke kan zarginsa da cin mutuncin manzon Allah a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Majalisar Dinkin Duniya Ta Bukaci a Saki Mubarak Bala Da Ake Zargi Da Batanci Ga Annabi
Majalisar Dinkin Duniya Ta Bukaci a Saki Mubarak Bala Da Ake Zargi Da Batanci Ga Annabi
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Malaman Addinin Kirista Sunyi Tattaki Na Goyon Bayan Pantami a Abuja

A cewar Kwararrun na Majalisar Dinkin Duniya, "Kame da tsarewar da aka yi wa Mr Bala take hakkin bin adama ne kuma hakan ya yi tasiri kan yancin walwala a Nigeria."

Sun nuna rashin jin dadinsu kan yadda mahukunta a Nigeria suka ki bin umurnin Babban Kotun Tarayya da ta bayar a ranar 21 ga watan Disamba na sakin Mr Bala.

Baya ga umurnin sakinsa, kotun har wa yau ta ce a biya shi diyyar N250,000 kan keta hakokinsa.

A ranar 20 ga watan Afrilun shekarar 2021 aka shirya sauraron karar sai dai an dage saboda yajin aikin da ma'aikatan shari'a ke yi a kasar.

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: FEC ta Amince a Fara Aiwatar Da Shirin Rage Talauci Na Ƙasa a Nigeria

Kwararrun na Majalisar Dinkin Duniya sun bukaci gwamnatin Nigeria da ta tabbatar da cewa an mutunta umurnin na kotu.

A wani rahoton daban, Mallam Garba Shehu ya caccaki wadanda suke sukar Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Dr Isa Pantami saboda rashin yafe masa abin da ya yi a baya, Channels Television ta ruwaito.

Ya na ganin rashin yafewa ministan kan maganganun da ya yi na goyon bayan kungiyoyi masu tsatsauran ra'ayi ya fi muni kan laifin da ministan ya aikata.

Babban mai taimakawa shugaban kasar a bangaren watsa labarai ya yi wannan kalaman ne a lokacin da ya bayyana a shirin Politics Today na Channels Television a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel