Buhari Ya Amince a Fara Aiwatar Da Shirin Rage Talauci Na Ƙasa a Nigeria

Buhari Ya Amince a Fara Aiwatar Da Shirin Rage Talauci Na Ƙasa a Nigeria

- Kwamitin Zartarwa na Tarayya, FEC, karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ya amince shirin rage talauci na kasa, NPRGS

- Wannan shirin na daga cikin shiryen-shiryen da zai taimakawa gwamnatin Buhari cika burinta na tsamo yan Nigeria miliyan daya daga talauci

- Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ne zai jagoranci kaddamar da manufofin shirin na rage talauci da habbaka kasa

Kwamitin zartarwa na kasa, FEC, ta amince da shirin rage talauci da habbaka kasa, NPRGS, da kwamitin bawa shugaban kasa shawara, PEAC, ta gabatar.

Femi Adesina, mashawarcin shugaban kasa na musamman kan kafafen watsa labarai ne ya bayyana hakan yayin jawabin da ya yi wa manema labarai a karshen taron mako-mako, a ranar Talata a Abuja.

DUBA WANNAN: 'Yan Bindiga Sun Buɗewa Ayarin Motocin Sanata Wuta a Kogi

Yanzu-Yanzu: Za a Fara Aiwatar Da Shirin Rage Talauci Na Ƙasa a Nigeria
Yanzu-Yanzu: Za a Fara Aiwatar Da Shirin Rage Talauci Na Ƙasa a Nigeria
Asali: Original

A watan Fabarairu, kwamitin bada shawarwarin da Doyin Salami ke yi wa jagoranci ta mika rahotonta ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Wannan shirin na daga cikin shiryen-shiryen da zai taimakawa gwamnatin Buhari cika burinta na tsamo yan Nigeria miliyan daya daga talauci cikin shekara 10.

Ya ce mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, wanda ke jagorantar PEAC, zai shugabanci kwamiti domin ganin an aiwatar da shirin yadda ya dace.

Adesina ya ce kwamitin na FEC ta kuma amince da aiwatar da shirin cikin tsarin matsakaicin zango da dogon zango na shirin cigaban kasa na 2021-2025 da ajanda 2050.

KU KARANTA: Malaman Addinin Kirista Sunyi Tattaki Na Goyon Bayan Pantami a Abuja

Har wa yau, kwamitin ta umurci ministan shari'a kuma antoni janar na kasa, Abubakar Malami ya shirya doka da za a gabatarwa majalisar tarayya domin ganin shirin ya dore.

A wani rahoton daban, Mallam Garba Shehu ya caccaki wadanda suke sukar Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Dr Isa Pantami saboda rashin yafe masa abin da ya yi a baya, Channels Television ta ruwaito.

Ya na ganin rashin yafewa ministan kan maganganun da ya yi na goyon bayan kungiyoyi masu tsatsauran ra'ayi ya fi muni kan laifin da ministan ya aikata.

Babban mai taimakawa shugaban kasar a bangaren watsa labarai ya yi wannan kalaman ne a lokacin da ya bayyana a shirin Politics Today na Channels Television a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164