'Yan Bindiga Sun Buɗewa Ayarin Motocin Sanata Wuta a Kogi

'Yan Bindiga Sun Buɗewa Ayarin Motocin Sanata Wuta a Kogi

- Yan bindiga sun kaiwa tawagar Sanata Clifford Ordia mai wakiltar Edo ta Tsakiya hari

- Dan majalisar da ayarin motocinsa na hanyarsu ta zuwa Abuja ne yan bindigan suka bude musu wuta a hanyar Okene zuwa Lokoja a jihar Kogi

- Yan sanda da ke tawagar dan majalisar sun dakile harin bayan musayar wuta amma uku sun jikkata

Yan sanda uku sun jikkata bayan yan bindiga sun budewa ayarin motocin Clifford Ordia, Sanata mai wakiltar Edo ta tsakiya wuta, The Cable ta ruwaito.

Harin ya faru ne a ranar Litinin a hanyar Okene zuwa Lokoja a jihar Kogi. Sanatan ya baro garinsu a jihar Edo ne yana hanyar komawa Abuja yayin da yan bindigan suka bude musu wuta.

Yan Bindiga Sun Budewa Ayarin Motocin Sanata Wuta a Kogi
Yan Bindiga Sun Budewa Ayarin Motocin Sanata Wuta a Kogi. Hoto: @daily_trust
Asali: Facebook

Da ya ke magana da manema labarai a ranar Laraba a Abuja, Ordia ya ce harin ya jefa shi cikin damuwa.

DUBA WANNAN: Fulani Buhari Ke Yi Wa Sharen Fage Domin Su Mamaye Nigeria, Ortom

"Na matukar shiga damuwa saboda faruwar lamarin," in ji dan majalisar.

"Muna dawowa daga jihar Edo, wani wuri tsakanin Okene da Lokoja, muka hadu da wasu da muke zargin yan bindiga ne. Suka bude wa ayarin motocci na wuta. Nan take yan sandan suka mayar musu da wutar.

"Motar jami'an tsaro da ke bayan mu suma sun budewa yan bindigan wuta suka yi nasarar dakile harin. Yayin musayar wutar yan sanda uku sun jikkata. Raunin daya daga cikinsu ya munana hakan yasa nan take muka kai shi Cibiyar Lafiya na Tarayya da ke Lokoja a jihar Kogi.

"Sun yi kokari sun basu kulawa. Zan kira Cibiyar Lafiya da ke Abuja domin daya daga cikin yan sandan akwai harsashi a jikinsa kusa da hantarsa."

KU KARANTA: Malaman Addinin Kirista Sunyi Tattaki Na Goyon Bayan Pantami a Abuja

Sanatan ya kuma ce sun hadu da wani tsaikon a kusa da Abaji inda wasu suka sake bude musu wuta amma sun dakile harin.

Sanatan na jam'iyyar PDP ya ce dole gwamnatin tarayya ta dauki mataki na kare lafiya da dukiyoyin mutane a kasar nan.

A wani rahoton daban, Mallam Garba Shehu ya caccaki wadanda suke sukar Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Dr Isa Pantami saboda rashin yafe masa abin da ya yi a baya, Channels Television ta ruwaito.

Ya na ganin rashin yafewa ministan kan maganganun da ya yi na goyon bayan kungiyoyi masu tsatsauran ra'ayi ya fi muni kan laifin da ministan ya aikata.

Babban mai taimakawa shugaban kasar a bangaren watsa labarai ya yi wannan kalaman ne a lokacin da ya bayyana a shirin Politics Today na Channels Television a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164