Majalisa Ta Tabbatar Da Salisu Garba a Matsayin Alƙalin Alƙalan Abuja
- Majalisar tarayya ta amince da nadin Salisu Garba a matsayin alkalin alkalan kotun birnin tarayya Abuja
- Salisu Garba ya kasance mukadashin alkalin alkalan kotun Abuja tun a watan Janairu bayan ritayar Ishaq Bello
- An tabbatar da nadin Salisu Garba ne bayan kwamitin shari'a na majalisa ta gabatar da bincike kansa inda ta ce ya cancanta
Majalisa ta tabbatar da nadin Salisu Garba a matsayin alkalin alkalai na kotun babban birnin tarayya, FCT, Abuja, The Cable ta ruwaito.
An tabbatar da nadin Garba ne a ranar Laraba bayan Opeyemi Bamidele, shugaban kwamitin shari'a na majalisar ya gabatar da rahoto kan wanda aka yi wa nadin.

Asali: Twitter
DUBA WANNAN: Malaman Addinin Kirista Sunyi Tattaki Na Goyon Bayan Pantami a Abuja
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar ta tabbatar da nadinsa tunda farko a watan Afrilu.
Garba, kasancewarsa ma'aikaci mafi girma a kotun shine ya rika aiki a matsayin mukadashin alkalin alkalan Abuja bayan ritayar Ishaq Bello a watan Janairu.
Yayin gabatar da rahotonsa, Bamidele ya ce wanda aka zaba din ya cika dukkan ka'idojin da ake bukata don haka a tabbatar da shi a matsayin alkalin alkalan kotun Abuja.
"Nadinsa ya zama dole biyo bayan ritayar Ishaq Bello. Bisa tanadin kudin tsarin mulki, tsohon alkalin alkalan ya yi ritaya a watan Janairu," in ji shi.
"Nadinsa ya yi dai-dai da tanadin sashi na 256(1) na kundin tsarin mulki. Nadinsa ya cika ka'idojin kundin tsarin mulki na shekarar 1999 da dokokin majalisa.
"Babu wanda ya shigar da kara kan wanda aka yi wa nadin."
KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: 'Yan Daba Sun Cinnawa Kotun Tarayya Wuta a Ebonyi
Daga bisani an tabbatar da nadin Garba bayan Shugaban Majalisa Ahmad Lawan ya yi kuri'a.
Sabon alkalin alkalan dan asalin karamar hukumar Malumfashi ne a jihar Katsina. Ya zama lauya a 1984 sannan ya kammala NYSC a 1985.
An nada shi majistare na babban kotun Abuja a 1989.
A 1997, ya zama Cif Rajistara na babban kotun Abuja, bayan shekara daya an nada shi alkalin kotun.
A wani rahoton daban, Mallam Garba Shehu ya caccaki wadanda suke sukar Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Dr Isa Pantami saboda rashin yafe masa abin da ya yi a baya, Channels Television ta ruwaito.
Ya na ganin rashin yafewa ministan kan maganganun da ya yi na goyon bayan kungiyoyi masu tsatsauran ra'ayi ya fi muni kan laifin da ministan ya aikata.
Babban mai taimakawa shugaban kasar a bangaren watsa labarai ya yi wannan kalaman ne a lokacin da ya bayyana a shirin Politics Today na Channels Television a ranar Juma'a.
Asali: Legit.ng