Da Duminsa: Hotunan Babban Kotun Tarayya da Ƴan Daba Suna Ƙona a Ebonyi

Da Duminsa: Hotunan Babban Kotun Tarayya da Ƴan Daba Suna Ƙona a Ebonyi

- 'Yan daba masu yawa sun kai hari babban kotun tarayya da ke Abakaliki a jihar Ebonyi

- Bayan haura katangar kotun, yan daban sunyi amfani da 'bam' din fetur sun bankawa kotun wuta

- Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Ebonyi, DSP Loveth Odah ta tabbatar da afkuwar harin

Wasu da ake zargin yan daba ne suna cinnawa wasu sassan kotun tarayya da ke Abakaliki jihar Ebonyi wuta, Daily Trust ta ruwaito.

Jami'an tsaro biyu sun jikkata sakamakon harin da aka kai a safiyar ranar Talata.

Majiyar Legit.ng ta gano cewa yan daban sun haura katanga kafin suka aikata mummunan harin.

DUBA WANNAN: 'Yan Bindiga Sun Afkawa Ayarin Motocin Sojoji Sun Kashe Huɗu

Yanzu-Yanzu: 'Yan Daba Sun Cinnawa Kotun Tarayya Wuta a Ebonyi
Yanzu-Yanzu: 'Yan Daba Sun Cinnawa Kotun Tarayya Wuta a Ebonyi. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

Yanzu-Yanzu: 'Yan Daba Sun Cinnawa Kotun Tarayya Wuta a Ebonyi
Yanzu-Yanzu: 'Yan Daba Sun Cinnawa Kotun Tarayya Wuta a Ebonyi. Hoto: @TheNationNews
Asali: UGC

An ce sunyi amfani da 'bam' din da ake hadawa da fetur domin kona kotun.

Sun kuma kona dakin karatu da ke kotun yayin da suka lalata dakunan jami'an tsaro.

Wakilin majiyar Legit.ng wanda ya ziyarci kotun a safiyar ranar Talata ya gano yan sanda da motocin sintiri guda uku a harabar kotun.

An gaza shiga cikin harabar kotun domin jami'an tsaro sun ce rajistara na kotun ya ce kada a bari kowa ya shiga idan ba ma'aikacin kotun bane.

KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: Boko Haram Ta Kafa Tuta a Ƙauyen Jihar Niger

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar DSP Loveth Odah ta tabbatar da afkuwar lamarin.

Odah ta ce yan daban da suka kai harin suna da yawa sosai.

Sai dai ta ce jami'an hukumar kashe gobara sun taimaka wurin kashe wutar.

"Yan daba masu dimbin yawa sun kona wasu sassan kotun amma masu kashe gobara sun zo cikin gaggawa sun kashe wutar," in ji ta.

Harin ya jefa mutane cikin damuwa hakan yasa jami'an tsaro suke cikin shirin ko ta kwana a jihar.

A yan kwanakin nan, yan bindiga suna ta kai wa hukumomin gwamnati hari a Kudu maso Gabashin Nigeria.

A wani rahoton daban, Mallam Garba Shehu ya caccaki wadanda suke sukar Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Dr Isa Pantami saboda rashin yafe masa abin da ya yi a baya, Channels Television ta ruwaito.

Ya na ganin rashin yafewa ministan kan maganganun da ya yi na goyon bayan kungiyoyi masu tsatsauran ra'ayi ya fi muni kan laifin da ministan ya aikata.

Babban mai taimakawa shugaban kasar a bangaren watsa labarai ya yi wannan kalaman ne a lokacin da ya bayyana a shirin Politics Today na Channels Television a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel