Kungiya ta bayyana 'makarkashiyar' da ta sa aka ki yin waje da Dr. Isa Pantami daga Gwamnati

Kungiya ta bayyana 'makarkashiyar' da ta sa aka ki yin waje da Dr. Isa Pantami daga Gwamnati

- Kungiyar MASSOB ta tabo Ministan sadaarwa, Isa Ali Ibrahim Pantami

- Shugaban MASSOB ya na zargin gwamnatin Buhari da shirin kafa daula

- Uchenna Madu ya ce za ayi amfani da Ministan domin ayi murdiyar zabe

A ranar Talata, 28 ga watan Afrilu, 2021, Punch ta ce MASSOB mai fafutuka domin samar da kasar Biyafara ta sa baki game da lamarin Dr. Isa Ali Pantami.

Kungiyar MASSOB ta ce tun farko shugaba Muhammadu Buhari ya nada Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami a matsayin Minista ne da nufin cin ma wani buri.

A cewar shugaban kungiyar, Uchenna Madu, an ba Isa Ali Ibrahim Pantami kujerar Ministan tarayya ne saboda a kafa daular musulunci da karfi da yaji.

KU KARANTA: Forum of Christian Bishops and Clergy Council su na tare da Pantami

Uchenna Madu ya na zargin gwamnatin tarayya da yunkurin kakaba Fulani kan al’umma, sannan a maida Najeriya ta zama wata daular musulunci a Afrika.

Madu yake cewa aikin Isa Ali Ibrahim Pantami shi ne ya tattara bayanan sadarwa na kafar zamani ta yadda Musulmai da Arewa za su tafka magudi a zabe.

Shugaban kungiyar ta MASSOB ya zargi Ministan sadarwa da bunkasa tattalin arzikin zamanin kasar da zama mai ra’ayin rikau a kan abin da ya shafi kabilanci.

A jawabin da ya fitar a jiya, Madu ya zargi Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami da yada ra’ayinsa na rikau tare da goyon bayan ta’addanci da sunan addininsa na musulunci.

KU KARANTA: Daga jiya zuwa yau, an kai hare-hare a garuruwa 15

Kungiya ta bayyana 'makarkashiyar' da ta sa aka ki yin waje da Dr. Isa Pantami daga Gwamnati
Buhari da Ministoci a taron FEC

“Pantami zai yi wa shugaba Muhammadu Buhari aiki da kyau a tunaninsa mara zurfi na ganin Najeriya ta zama kakarkashin Fulani a Afrika ta yamma.” Inji sa.

Madu ya ce “A yankin kudu da arewa ta tsakiya inda kiristoci su ka fi yawa ne kurum Dr. Pantami ya wajabta wa mutane yin rajistar katin zama ‘dan kasa na NIN.”

“Pantami ba zai taba murabus ba, zai taimaka wa Buhari wajen ganin Najeriya ta zama kasar Fulani."

A makon nan aka ji Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, ya zargi Shugaba Muhammadu Buhari da yi wa fulani sharen fage domin su karbe mulkin kasa.

Gwamna Ortom ya bayyana hakan ne yayin jawabin da ya yi a ranar Talata a kan kisar da ake zargin makiyaya sun yi, ya ce halin yanzu doka ba ta aiki a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel