Fulani Buhari Ke Yi Wa Sharen Fage Domin Su Mamaye Nigeria, Ortom
- Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya yi zargin Shugaba Buhari Fulani kawai ya ke yi wa aiki
- Gwamna Ortom ya yi wannan zargin ne yayin da ya ke jawabi kan kisar da aka yi wa wasu mutane a Benue
- Ortom ya kara da cewa mutanen jihar Benue sun gaji da irin wannan kisar da ake musu kuma gwamnatin tarayya ta gaza daukar mataki
Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya zargi Shugaban kasa Muhammadu Buhari da yi wa fulani sharen fage domin su mamaye Nigeria, The Punch ta ruwaito.
Ortom ya bayyana hakan ne yayin jawabin da ya yi a ranar Talata kan kisar da ake zargin makiyaya fulani ne suka yi a sassan yankin Arewa ta Tsakiya.
DUBA WANNAN: 'Yan Boko Haram Sun Zaƙewa Matan Aure a Niger Bayan Sun Musu Girki Sun Cinye
Ya kuma koka kan cewa a kalla mutane 70 ne aka kashe cikin makonni biyu da suka gabata a kananan hukumomi uku a jihar.
Gwamnan, wanda ya ce ba zai yi wu a cigaba da kashe-kashen ba ya ce, "Menene ke faruwa yanzu, ni dai, abin a fili ya ke, Shugaban kasa yana yi wa Fulani aiki ne domin su karbe kasar baki daya."
Ya cigaba da cewa alama da ya ke gani daga Shugaban kasar ta rashin daukan matakan da suka dace ya nuna cewa shi shugaba ne kawai na Fulani duk da ya dade da sanin haka.
KU KARANTA: Karin Bayani: Bidiyon Ɗaliban Kaduna Da Ke Hannun Ƴan Bindiga Tsawon Kwanaki 47
"Muna sauyawa zuwa kasa mara doka, idan muna da shugaban kasa da ya bawa jami'an tsaro umurnin su harbe duk wanda suka gani da AK-47 sannan ministan tsaro ya fito ya ce ba za su iya harbi hakan nan ba ... toh, wanene kwamandan rundunar sojoji na kasar?," in ji Ortom.
A cewar gwamnan, ana neman kure mutanen Benue saboda irin hare-haren da ake kai musu.
A wani rahoton daban, Mallam Garba Shehu ya caccaki wadanda suke sukar Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Dr Isa Pantami saboda rashin yafe masa abin da ya yi a baya, Channels Television ta ruwaito.
Ya na ganin rashin yafewa ministan kan maganganun da ya yi na goyon bayan kungiyoyi masu tsatsauran ra'ayi ya fi muni kan laifin da ministan ya aikata.
Babban mai taimakawa shugaban kasar a bangaren watsa labarai ya yi wannan kalaman ne a lokacin da ya bayyana a shirin Politics Today na Channels Television a ranar Juma'a.
Asali: Legit.ng