Munanan hare-hare 13 da ‘Yan bindiga da ‘Yan Boko Haram su ka kai a sa’a 48 da su ka wuce

Munanan hare-hare 13 da ‘Yan bindiga da ‘Yan Boko Haram su ka kai a sa’a 48 da su ka wuce

Wannan makon ya na cikin mafi muni da aka shiga a cikin ‘yan shekaru a Najeriya saboda irin yadda ‘yan bindiga su ke ta faman kai hare-hare.

Legit.ng Hausa ta tattaro maku jerin hare-haren da aka kai a garuruwan kasar nan daga ranar Litinin, 26 ga watan Afrilu, 2021, zuwa yau Talata.

1. Kaduna

A garin Kaduna, bayan hare-haren da aka kai a Jami’ar Greenfield da wani coci, an sake samun wasu gawawwaki na wasu daga cikin ‘daliban wannan jami’a da aka sace a kwanakin baya.

2. Zaria

‘Yan bindiga sun dura Zaria cikin dare sun yi garkuwa da wasu mutane hudu bayan an yi ba-ta-kashi. ‘Yan banga da jami’an tsaro sun cafke mutum biyu daga cikin masu satar mutanen.

3. Imo

A Imo, an samu ‘yan bindiga sun auka wa ofishin ‘yan sanda, su ka kashe manyan jami’ai biyar, sannan su ka banka wa ofishin jami’an tsaron wuta. A baya an kashe wani kwamishina.

4. Neja

‘Yan Boko Haram sun shiga jihar Neja, har sun kafa tuta a yankin Shiroro kamar yadda gwamnati ta tabbatar. ‘Yan ta’addan sun yi wa mata fyade, kuma sun yi gaba da iyalan Bayin Allah.

KU KARANTA: Jirgin yaƙin sojojin sama ya hallaka sojojin kasa 33 a Mainok

5. Kebbi

Abin da ya faru da wasu jami’an ‘yan sanda a Kebbi bai yi dadi ba. ‘Yan bindiga sun hallaka wani DPO, sannan su ka kashe ‘yan sanda takwas da wasu ‘yan sa-kai akalla mutum biyu.

6. Borno

A lokacin da ake jin labarin cewa mutane ke tserewa daga wasu yankunan sai aka ji ‘Yan ta’addan Boko Haram sun kai wa Gwoza hari. Kafin nan an rasa sojojin kasa da-dama a Mainok.

7. Osun

Rahotanni sun tabbatar da cewa an sace wasu matafiya uku a jihar Osun. Yanzu haka ‘yan sanda da jami’an sa-kai su na ta faman zagaye jeji domin su gano wadannan Bayin Allah.

8. Anambra

Mutane tara ake zargin sun mutu yayin da aka kai wa wasu makiyaya hari a Anambra. Kafin nan an kona fadar Mai martaba Igwe Ifitedunu da ke yankin karamar hukumar Dunukofia.

9. Legas

A Legas an ji harbe-harbe a wani yanki, hakan ya jawo ake rade-radin ana rikici tsakanin Hausawa da Yarbawa. Amma Legit.ng Hausa ta tabbatar da ba rikicin kabilanci ake yi ba.

KU KARANTA: Boko Haram sun dura garin Geidam, sun yi ta'adi

Munanan hare-hare 13 da ‘Yan bindiga da ‘Yan Boko Haram su ka kai a sa’a 48 da su ka wuce
Hafsoshin tsaro a fadar shugaban kasa
Asali: Twitter

10. Ribas

Ana zargin dakarun kungiyar IPOB masu rajin samar da kasar Biyafara da laifin kashe sojojin Najeriya hudu a Ribas. Sojojin kasan su na aiki ne a karkashin wani kamfanin mai.

11. Oyo

Wasu mutane da ba a sa su wanene ba, sun kai hari gidan Sunday Igboho a garin Ibadan, amma ba su yi nasarar kama shi ba. An ji harbe-harben bindiga yayin da aka kai wannan hari.

12. Ebonyi

A farkon wannan makon aka ji cewa ‘yan bindiga sun kona babban kotun tarayya a Ebonyi. Wannan ya na cikin hare-haren da aka kai a yankin Kudu maso gabashin Najeriya.

13. Nasarawa

A Nasarawa da ke yankin Arewa maso tsakiya an kai wa wadanda ke sansanin gudun hijira hari. A sanadiyyar haka mutane su ka fito su ka yi zanga-zanga a titin Benuwai-Nasarawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng