Pantami: Ministan da aka taso gaba, ya fallasa sabuwar makarkashiyar da ake kitsa masa

Pantami: Ministan da aka taso gaba, ya fallasa sabuwar makarkashiyar da ake kitsa masa

- Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami ya ce akwai danyen tuggun da ake ta shirya masa

- Ministan ya bayyana cewa ana yunkurin wallafa wasu bidiyoyin bogi a kansa

- Pantami ya ja-kunnen masu wannan shiri, ya ce ba zai bari a bata sunansa ba

Ministan sadarwa da bunkasa tattalin arzikin zamani, Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami, ya bayyana cewa akwai wani tuggun da ake yunkurin shirya masa.

Jaridar Punch ta ce Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami ya yi wannan bayani ne a ranar Litinin, 26 ga watan Afrilu, 2021, ta bakin hadimarsa, Uwa Suleiman.

Mai taimaka wa Ministan wajen yada labarai, Uwa Suleiman, ta fitar da jawabi, ta na bayanin makarkashiya na gaba da aka shirya wa mai gidanta.

KU KARANTA: Muhimman abubuwa 5 da Buhari ya fada wajen wanke Pantami

A cewar Ministan, yanzu abin da ya rage shi ne a fito da bidiyoyi na karya da aka hada domin a cin ma burin da ake da shi na ganin an goga masa kashi.

Ga abin da jawabin ya ce:

“Mu na da ingantaccen bayanan sirri cewa wasu da su ke ta fadi-tashi, su na yaki da Pantami, za su koma wa makarkashiya na gaba a wannan aikin na su.”

“Wannan karo, miyagun su na neman wadanda za su yi masa dako, su fito da bidiyoyin bogi da za su nuna Ministan a wani irin yanayi domin bata masa suna.”

“Sam ba mu yi mamakin wannan sabon shiri ba, wanda ya nuna yadda su ka dage da karfi da yaji bayan a baya sun gaza samun nasarar ci wa Ministan mutunci.”

KU KARANTA: Gwamna ya na yi wa Sarakunan jihar Imo barazanar tsige su

Pantami: Ministan da aka taso gaba, ya fallasa sabuwar makarkashiyar da ake kitsa masa
Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami
Asali: Twitter

Mai girma Ministan tarayyar ya ce ya sanar da jama’a wannan danyen aiki ne tun wuri domin a ankara da abin da wadannan miyagun mutane su ke shirya masa

Pantami ya ce ba zai zauna wasu ‘yan-kora su yi kokarin bata masa suna a matsayinsa na shugaban al’umma, masanin addini, kuma jami’in gwamnati ba.

A jawabin da aka fitar da yawun bakin Ministan, ya gargadi masu wannan shiri da cewa su yi hattara da abin da zai iya zuwa ya dawo a sakamakon aikin na su.

Jiya ne fitattacen malamin addinin Islaman nan, Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana ra'ayinsa kan yadda aka hurowa ministan sadarwan Najeriya, Isa Pantami, wuta.

Malamin ya bayyana cewa Ministan ba 'dan ta'addani, sannan ya ce idan aka tube Isa Ali Pantami daga matsayinsa, 'yan Najeriya zasu yi matukar dana-sani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel