Muhimman abubuwa 5 da Shugaba Buhari ya fada a jiya wajen kare Ministansa, Pantami
Ku na da labari cewa fadar shugaban kasa ta fito ta kare Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr. Isa Ali Pantami daga zargin masu zargi.
Mai girma shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya yi jawabi ta bakin hadiminsa, Garba Shehu, inda ya nuna cikakken goyo baya ga Ministan.
A jawabin da aka fitar a maraicen ranar Alhamis, za a iya gane cewa babu yunkurin tsige Ministan, sannan ana zargin ‘yan siyasa ne su ka huro masa wuta.
Legit.ng ta yi wa jawabin shugaban kasar fida, inda ta bi abin da Garba Shehu ya fada daki-daki:
1. Bata suna
A wajen gwamnatin Muhammadu Buhari, kiran da ake yi na sauke Isa Pantami daga kujerar Minista ba komai bane illa kokarin bata masa suna, ci masa mutunci, da kassara shi.
KU KARANTA: A daina danganta mutuwar Yakowa da Isa Pantami - CAN
2. A bar tuna baya
Fadar shugaban Najeriya ta ce a daina dawo da abin da ya riga ya wuce na abin da malamin addinin ya furta a lokacin ya na wa’azi shekarun baya, tun da ya tuba, ya nemi afuwa.
“Ministan ya bada hakuri na abin da ya faru a 2000. Ba za a karbi wadannan maganganu ba ko yau idan zai maimata su, amma ba zai maimaita su ba, ya sauka daga matsayin nan.”
3. Ya na matashi ne…
Garba Shehu ya ce akwai yarunta a lokacin: “A shekarun 2000, Ministan ya na shekara 20-da-‘yan kai; badi zai cika 50. An sha miya yanzu, kuma mutane su na canza ra’ayinsu.”
4. A rika yin adalci
Shugaban kasar ya yi kira ga mutanen Najeriya su zama masu adalci wajen mu’amala da kowa. Garba Shehu ya ce bai kamata a rika wuce gona da iri wajen hulda da mutane ba.
KU KARANTA: Duk Musulmin da ya biye wa masu sukar Pantami ‘Wawa’ ne - Mansur Sokoto
5. Sharrin ‘yan siyasa ne
Wani ikirarin da fadar shugaban kasar ta yi shi ne ‘yan siyasa ke yi wa Ministan tuggu. Ya ce bayanai na nuna ‘yan adawa su ka taso Ministan ta hannun kamfanonin sadarwa.
A jiya kun ji fadar shugaban kasar Najeriya ta mayar da martani game da zargin cewa ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr. Isa Ali Pantami, ya na tare da 'yan ta'adda.
A cewar mai magana da bakin shugaban kasa, a halin yanzu Isa Pantami ya na fuskantar tirjiya wanda wasu da ke neman a tsige shi, duk da gudumuwar da ya ba gwamnati.
Asali: Legit.ng