Gwamnan APC ya na yi wa Sarakunan jiharsa barazanar tsige su saboda matsalar tsaro

Gwamnan APC ya na yi wa Sarakunan jiharsa barazanar tsige su saboda matsalar tsaro

- Gwamna Hope Uzodinma ya yi kira ga Sarakuna su dage a kan sha’anin tsaro

- Hope Uzodinma ya ce zai tunbuke Sarkin da ya kyale zubar da jinin al’umma

- Gwamnatin Imo ta bukaci shugabanni su bada hadin-kai domin a samu tsaro

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Mai girma gwamnan Imo, Hope Uzodinma, ya na barazanar sauke duk wani mai sarauta da ya bari ana kashe-kashe a kasarsa.

Gwamnan ya bayyana cewa dole sarakunan gargajiyan jihar Imo su tashi su yi abin da ya dace domin ganin an samu zaman lafiya a gundumomin da su ke riko.

“Gwamnatin jihar Imo ta dauki matakin tsige duk wani Sarki da ya ki yin wani abu yayin da ake fama da matsalar rashin tsaro a kasar da yake sarauta.” Inji shi.

KU KARANTA: Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana dalilin daina zama da 'yan bindiga

Sanata Hope Uzodinma ya yi wannan jawabi ne a garin Owerri, jihar Imo, a wajen wani taro da aka yi kan harkar tsaro a ranar Alhamis, 22 ga wtan Afrilu, 2021.

Wadanda su ka samu halartar wannan taro sun hada da sabon mataimakin shugaban sufeta janar na ‘yan sanda da aka kawo yankin Imo da kewaye, Ekim Okon.

Mataimakin gwamnan jihar Imo, Farfesa Placid Njoku, ne ya wakilci mai girma gwamna wajen zaman.

A madadin gwamna, Placid Njoku, ya yi kira ga shugabannin kungoyin kiristoci, ‘yan kwadago, dalibai da ‘yan kasuwa, su hada kai da gwamnatin APC a jihar Imo.

Gwamnan APC ya na yi wa Sarakunan jiharsa barazanar tsige su saboda matsalar tsaro
Gwamnan Jihar Imo, Sanata Hope Uzodinma
Asali: Facebook

KU KARANTA: 'Yan siyasar kasar Inyamurai da za su iya takarar Shugaban kasa a 2023

Hope Uzodinma ya bukaci wadannan kungiyoyi su hada kai da shi domin ganin an samu zaman lafiya.

Ya ce: “Sha’anin tsaro ya na cikin abubuwan da Uzodinma ya dauka da muhimmanci tun da ya samu mulki. Harkar tsaro ba ta da takwara, dole mu tsare jihar Imo.”

“Dole ya zamana Sarki zai iya magance rashin tsaro a kasarsa. Kula da masu shige da fice babban aikinsa ne. Idan Sarakuna su ka yi aikinsu, za a samu zaman lafiya.”

A jiya aka ji Ministan tsaro na kasa, Janar Bashir Magashi ya na cewa mutuwar shugaban kasar Chadi, Idris Deby, matsala ce ga kasar Najeriya da sauran makwabta.

Gwamnatin tarayya ta ce kashe Shugaban Chad zai taba Najeriya sosai. A sakamakon kisan Shugaba Idris Deby, Ministan ya ce su na kara sa ido a kan iyakokinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng