Da ɗuminsa: NBC ta dakatar da Channels TV tare da tarar N5m

Da ɗuminsa: NBC ta dakatar da Channels TV tare da tarar N5m

- Hukumar NBC ta dakatar da gidan talabijin na Channels Television tare cinta tarar Naira miliyan 5

- NBC ta ce Channels Television ta yi hira da shugaban IPOB inda ta bari yana ta furta kalaman da suka saba dokoki aiki

Hukumar da ke kula da kafafen watsa labarai a Nigeria, NBC, ta dakatar da gidan talabijin na Channels Television daga watsa shirye-shirye saboda saɓa dokokinta.

Kazalika, an kuma ci gidan talabijin cin tarar Naira miliyan 5.

DUBA WANNAN: Da Ɗuminsa: Ƴan IPOB Sun Yi Wa Makiyaya Fulani 19 Yankan Rago a Anambra

Da ɗuminsa: NBC ta dakatar da Channels TV tare da tarar N5m
Da ɗuminsa: NBC ta dakatar da Channels TV tare da tarar N5m. Hoto: @thecableng
Asali: UGC

A cikin wasikar da NBC ta aika wa shugaban Channels Television mai ɗauke da sa hannun shugabanta Armstrong Idachaba, hukumar ta ce an dauki matakan ne saboda shirin kai tsaye da ta watsa misalin ƙarfe 7 na yamma ranar Lahadi 25 ga watan Afrilun 2021.

A cewar NBC, gidan talabijin ɗin ta saba doka saboda bawa shugaban kungiyar masu fafutikar kafa kasar Biafra, IPOB, ta furta kalamun ɓallewa daga ƙasa da tada rikici ba tare da yi masa gyara ko gargaɗi ba.

KU KARANTA: Jiragen Yaƙin NAF Sun Jefa Wa Sojojin Ƙasa Bam Bisa Kuskure

Mista Armstrong ya ƙara da cewa hakan ya saba wa dokokin watsa labarai.

Ta kuma zargin gidan talabijin ɗin da barin baƙonta ya furta kalaman cin mutunci, ƙarya kan Rundunar sojojin Nigeria duk da cewa kotu ta haramta kungiyar.

A wani rahoton daban, Mallam Garba Shehu ya caccaki wadanda suke sukar Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Dr Isa Pantami saboda rashin yafe masa abin da ya yi a baya, Channels Television ta ruwaito.

Ya na ganin rashin yafewa ministan kan maganganun da ya yi na goyon bayan kungiyoyi masu tsatsauran ra'ayi ya fi muni kan laifin da ministan ya aikata.

Babban mai taimakawa shugaban kasar a bangaren watsa labarai ya yi wannan kalaman ne a lokacin da ya bayyana a shirin Politics Today na Channels Television a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel