Da Ɗuminsa: Boko Haram sun fara kafa tutocin su a wasu sassan Geidam
- Mayaƙan Boko Haram sun fara kafa tutocinsu a wasu yankunan ƙaramar hukumar Geidam, kwana biyu da kai harin su garin
- Har yanzun dai mayakan basu bar yankin ba duk kuwa da cewa bataliyar sojojin yankin na nan a yankin, amma hakan baisa sun daina abinda suke ba
- Yan ta'addan sun lalata kayan sadarwa a yankin, wanda hakan yasa ba damar amfani da kamfanonin sadarwa
Rahotannin dake shigowa yanzun sun nuna cewa mayaƙan Boko Haram sun fara kafa tutar su a wani ɓangare na Geidam, jihar Yobe.
KARANTA ANAN: Gwamnonin Arewa sun bayyana matakin da zasu ɗauka kan kisan ɗaliban jami'ar Greenfield
Wannan na zuwa ne bayan kwana biyu da yan ta'addan suka kai hari yankin ƙaramar hukumar Geidam.
Garin na Geidam shine mahaifar muƙaddashin sufetan yan sandan ƙasar nan, Mr. Usman Alƙali Baba.
Wasu daga cikin mazauna garin sun tabbarwa Channels tv cewa yan ta'addan sun kafa tutocinsu a wasu sassan garin.
Hakanan kuma, sun fara yawo gida-gida suna kiran mutane su yarda su amshi aƙidarsu.
KARANTA ANAN: Haɗa Miliyan N800m Ba Abune Mai Sauƙi Ba, Iyayen Ɗaliban Greenfield Sun Koka
Duk da cewa rundunar sojoji dake Geidam ɗin suna nan a yankin, amma hakan baisa yan ta'addan sun daina abinda suke yi ba.
Wasu daga cikin kafofin sadarwar yankin sun sami matsala saboda harin, wanda hakan ya kawo matsalar sadarwa a gaba ɗaya yankin.
Da yawa daga cikim mutanen yankin sun shiga halin ƙaƙa-ni-kayi saboda sun kasa samun damar ji daga yan uwansu saboda matsalar sadarwa a garin.
A wani labarin kuma Masallacin An-Noor dake Abuja Ya Tara Biliyan N1.3bn Domin Yin Wani Muhimmin Aiki
Cibiyar inganta addinin musulunci (ICICE) ta bayyana cewa an samu 1.3 biliyan daga cikin 3.15 biliyan da ake nema don kara fadada masallacin An-Noor
Shugaban cibiyar Dr. Kabir Kabo, shine ya bayyana haka ranar Asabar a Abuja , kuma yace za'a fara aikin bada jimawa ba.
Asali: Legit.ng