Haɗa Miliyan N800m Ba Abune Mai Sauƙi Ba, Iyayen Ɗaliban Greenfield Sun Koka

Haɗa Miliyan N800m Ba Abune Mai Sauƙi Ba, Iyayen Ɗaliban Greenfield Sun Koka

- Iyayen ɗaliban da aka sace a jami'ar Greenfield dake jihar Kaduna sun roƙi gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Kaduna su taimaka musu wajen kuɓutar da yayansu

- Ɗaya daga cikin iyayen ta bayyana cewa ɗanta ya koma makaranta ranar Talata, amma sai labarin sace shi taji ranar Laraba

- A wani taro da suka yi a Kaduna, iyayen sunce ba zasu iya haɗa waɗannan maƙudan kuɗaɗen da yan bindiga suka nema ba

Iyayen ɗaliban da aka sace a jami'ar Greenfield dake jihar Kaduna sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta Kaduna su taimaka musu wajen kuɓutar da 'yayansu.

KARANTA ANAN: Masallacin An-Noor dake Abuja Ya Tara Biliyan N1.3bn Domin Yin Wani Muhimmin Aiki

Wannan kiran na iyayen na zuwa ne bayan awanni 24 da hukumomin tsaro suka gano gawarwakin uku daga cikin ɗaliban da aka sace a jami'ar.

Wani taro da suka gudanar a Kaduna, iyayen sunce suna jin tsoron akashe musu yayansu matuƙar basu biya miliyan N800m kuɗin fansa ba, kamar yadda yan bindigan suka buƙata.

Wata mahaifiya da ɗanta ke cikin waɗanda aka sace ta bayyana cewa ɗanta ya koma makaranta ranar Talata, ta samu labarin an sace shi ranar laraba.

"Wannan abun ban tsoro ne, na kasa bacci, na kasa cin abinci; ina roƙon jama'a su taimaka mana. Ba zamu iya ɗaukar buƙatar yan bindigar ba, kuɗin sun wuce tunani." inji matar.

Haɗa miliyan N800m ba abune mai sauƙi ba, Iyayen ɗaliban Greenfield sun Koka
Haɗa miliyan N800m ba abune mai sauƙi ba, Iyayen ɗaliban Greenfield sun Koka Hoto: gfu.edu.ng
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Yan Sanda sun damƙe mutane huɗu da zargin kashe wani Sabon ango kwana ƙaɗan kafin bikinsa

Wani daga cikin iyayen mai suna, Markus Zarmai, yace babu ta yadda za'ai su iya biyan waɗannan maƙudan kuɗaɗen, kamar yadda Channels TV ta ruwaito

"80 miliyan ba wasa bane, matuƙar mutane basu taimaka mana ba, to bansan tayadda zamu iya haɗa wannan kudin ba." inji Markus.

Amma wani malamin coci, Rabaran Mathew Ndagoso, ya ƙarfafa ma iyayen gwuiwa, inda yace musu kada su karaya, su cigaba da roƙon gwamnati ta shigo lamarin.

"Ba zamu taɓa karaya ba, mu mutane ne masu ƙarfin gwuiwa da fata nagari. Zamu cigaba da karfafama mutane gwuiwa, kada su cire rai, zamu cigaba da faɗa ma gwamnati tazo tayi abinda ake buƙata.' injishi.

A wani labarin kuma Wata Mata ta mare ni a gaban mijinta bance komai ba, ɗan sandan da gwamnan Lagos ya karrama

Wani jami'in ɗan sanda mai suna, Sunday Erhabor, ya bayyana wasu manyan ƙalubalen da ya taɓa fuskanta a lokacin yana cikin aiki

Ɗan sandan yasha lambar yabo daga wajen gwamnan jihar Lagos saboda halin dattako, hakuri da juriya da ya nuna a lokacin da wani mai laifi ya ci mutuncinsa a yankin Oniru na jihar Lagos.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262