COVID-19: Gwamnatin ta ce ta raba tallafi amma mutane basu gani a kas ba, CODE

COVID-19: Gwamnatin ta ce ta raba tallafi amma mutane basu gani a kas ba, CODE

- An zargi gwamnatin tarayya da rashin daidai yayin rabon kayan tallafin Korona

- Wani dan fafutuka, Hamzat Lawal, ya baiwa gwamnati shawara kan yadda ya kamata ace tayi rabon tallafi

- A cewarsa, gwamnati na ikirari ta kashe makudan kudade amma mutanen basu gani ba

Shugaban kungiyar Connected Development CODE, Hamzat Lawal, ya soki yadda gwamnatin tarayya ta raba kayan tallafin annobar Korona.

Kungiyar Connected Development CODE, wata kungiya ce wacce ke kokarin taimakawa talakawa marasa galihu a nahiyar Afrika.

Hamzat ya ce yan Najeriya kawai labarin tallafin suke ji a Talabijin da rediyo amma basu gani a kas ba.

Ya bayyana hakan ne yayin hira da manema labarai a taron fayyace gaskiya kan yadda lamarin Korona, da kungiyar ta shirya tare da hadin kan BudgIT a Abuja.

DUBA NAN: Munanan hare-hare, garkuwa da mutane, da kashe-kashe 6 da suka auku jiya Laraba

COVID-19: Gwamnatin ta ce ta raba tallafi amma mutane basu gani a kas ba, CODE
COVID-19: Gwamnatin ta ce ta raba tallafi amma mutane basu gani a kas ba, CODE Photo: Connected Development
Asali: Facebook

DUBA NAN: Sai kun kara mana kudi zamu iya kawar da yan ta'adda, Shugaban Hafsan Soji Attahiru

Ya ce wasu yan Najeriyan da aka yi ikirarin baiwa tallafin dubu biyar-biyar ba haka aka basu ba, wasu jamian gwamnati sun zaftare kudin.

Hamza ya ce abinda ya kamata gwamnati tayi shine ta turawa mutane kudin ta asusun bankinsu ba yawon da kudade a jakunkuna.

"Ta yaya zaku cirebiliyoyi daga banki ku rike a hannu, sannan ku rika baiwa mutane a hannu, shin wannan cigaba ne ko cibaya? Amfani da fasahar zamani ya fi sauki," Hamza yace.

A bangare guda, Najeriya na bukatar sama da naira tiriliyan guda domin yaki da zazzabin cizon sauro a kasar, in ji Dokta Osagie Ehanire, gidan Talabijin na Channels ta ruwaito.

Ya bayyana cewa daga cikin jimillar kudin, kasar na bukatar sama da naira biliyan 350 don yaki da cutar a shekarar 2021 kadai.

Ehanire, Ministan Lafiya, ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a wani taron manema labarai a babban birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel