Sai kun kara mana kudi zamu iya kawar da yan ta'adda, Shugaban Hafsan Soji Attahiru

Sai kun kara mana kudi zamu iya kawar da yan ta'adda, Shugaban Hafsan Soji Attahiru

- Kwamitin majalisar dattawa da Sifeto Janar na yan sanda sun kai ziyara na musamman hedkwatar Sojin Najeriya

- Ana kokarin hada karfi da karfe wajen kawo karshen matsalar tsaro

- Hukumar Soji ta bukaci karin kudi don siyan makamai da kayan aiki

Shugaban Hafsoshin Soji, Laftanan Janar Ibrahim Attahiru, ya bayyanawa majalisar dattawa cewa a kara musu kudi don siyan makamai da kayan yaki.

Attahiru, ya bayyana hakan ne ranar Laraba yayinda ya karbi bakuncin kwamitin majalisar dattawa kan hukumar Soji a ofishinsa dake birnin tarayya Abuja, rahoton TheCable.

Ya ce hukumar na bukatar goyon bayan kwamitin don kawar da dukkan matsalolin tsaron kasar nan.

Attahiru ya ce Najeriya na fuskantar matsalolin tsaro da dama wanda ya hada da ta'addanci a Arewa maso gabas, barandanci a Arewa maso yamma da maso tsakiya, da kuma masu yunkurin ballewa daga a Najeriya a yankin Kudu maso gabas.

"Domin kawar da wadannan barazanan, hukumar Soji na bukatan kayan aiki, makamai, motocin yaki, da sauran abubuwan da zasu taimaka," yace.

"Ina kira gare ku cikin gaggawa, ku duba bukatar nan lokacin da kuke rabon kudaden kasafin kudin."

Ya tabbatarwa kwamitin cewa hukumar Sojin a karkashinsa ba zata shiga siyasa ba.

DUBA NAN: Rikicin PDP: Bangaren Kwankwaso sun dau fansa, an dakatar da Sanata Gwarzo

Sai kun kara mana kudi zamu iya kawar da yan ta'adda, Shugaban Hafsan Soji Attahiru
Sai kun kara mana kudi zamu iya kawar da yan ta'adda, Shugaban Hafsan Soji Attahiru Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

KU KARANTA: Munanan hare-hare, garkuwa da mutane, da kashe-kashe 6 da suka auku jiya Laraba

A bangarensa, shugaban kwamitin da suka kai ziyara, Ali Ndume, ya bayyana cewa sun kawo wannan ziyara ne domin fahimtar matsaloli da bukatun hukumar Sojin da kuma hanyar magancesu.

"Shiyasa muke kira ga gwamnati ta baiwa Sojoji kayan aikin da suke bukata wajen gudanar da aikin da ya rataya a kansu," yace.

A baya kun ji cewa Sojojin rundunar Operation Lafiya Dole sun gudanar da zanga-zanga kan turasu faggen yaki da 'yan ta'addan Boko Haram.

A cewar majiyoyi daga barikin Maimalari, Sojojin sun mamaye hedkwatar Operation Lafiya Dole ne a daren Alhamis suna harbin bindiga sama.

Sun bayyana cewa suna zanga-zanga ne sakamakon rashin biyansu alawus da kuma rashin isassun makaman yaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel